Tsohuwar Minista Ta Jero Tambayoyin da Ya Zama Wajibi JAMB Ta Amsa Kan Rudanin Mmesoma

Tsohuwar Minista Ta Jero Tambayoyin da Ya Zama Wajibi JAMB Ta Amsa Kan Rudanin Mmesoma

  • Obiageli Ezekwesili ta ce akwai tulin tambayoyin da ya kamata JAMB ta amsa dangane da sakamakon jarabawar Mmesoma Ejikeme
  • Tsohuwar Ministar ilimi a Najeriya ta jaddada cewa tana nan a kan bakarta cewa a gudanar da bincike mai zaman kansa domin tono gaskiya
  • Ezekwesili ta kara da cewa ruɗanin sakamakon ɗalibar ya ƙara nuna cewa akwai buƙatar JAMB, ɗalibai da sauran al'umma su tashi tsaye

Tsohuwar ministar ilimi a Najeriya, Obiageli Ezekwesili, ta jero tambayoyin da ya zama tilas hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu (JAMB) ta fito ta amsa.

Ta ce ya zama kusan wajibi JAMB ta ba da amsoshin tambayoyin domin fayyace gaskiya kan ruɗanin da ke kewaye da sakamakon jarabawar UTME na Mmesoma Ejikeme.

Obiageli Ezekwesili da shugaban JAMB.
Tsohuwar Minista Ta Jero Tambayoyin da Ya Zama Wajibi JAMB Ta Amsa Kan Rudanin Mmesoma Hoto: Obiageli Oby Ezekwesili, Prof Ishaq O. Oloyede
Asali: Facebook

Misis Ezekwesili ta bayyana haka ne ranar Laraba, 5 ga watan Yuli, 2023 a shafinta na dandalin sada zumunta Tuwita.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, Ɗalibar da Ake Zargin Ta Yi Maguɗin Sakamakon JAMB Ta Faɗi Gaskiyar Makin da Ta Ci

Haka zalika ta jaddada cewa tana nan kan bakarta na kira da a gudanar da binciken fasaha mai zaman kansa domin bankaɗo ainihin gaskiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarta, wannan binciken zai taka rawa wajen bankaɗo abinda ya faru da kuma rawar da kowane ɓangare ya taka.

Ta ƙara da cewa abinda ya faru da ɗalibar da ake zargi ya ƙara fito da buƙatar ƙara neman ilimi mai zurfi ga ɗalibai, JAMB da ɗaukacin 'yan Najeriya.

Tsohuwar ministar ta jero tambayoyi kamar haka:

  • Menene gaskiya abinda aka ƙulla da har ya samar da sakamakon da Mmesoma Ejikeme ta yi ikirari?
  • Shin sauran mutane zasu amfana da matakan da Mmesoma ta bi?
  • Shin wannan tangarɗar ta sakamako biyu ita kaɗai ya shafa kon kuwa sauran ɗalibai da suka zauna JAMB/UTME sun fuskanci kwatankwacin haka?
  • Shin bincika baki ɗaya na'ura ba shi ne mafita ga JAMB ba a yanayi irin wannan kuma an aiwatar da hakan?
  • Wace irin alaƙa ke akwai tsakanin na'urar tattara bayanan JAMB da cibiyar zana jarabawan da ɗalibar da zauna jarabawar bana da kuma duba sakamako?
  • Ko wannan kes din da ya faru zai iya taimaka wa JAMB ta bi diddigin duk wani yunkurin da zai dakushe gaskiyar tsarin jarabawar?
  • Ta ya Mmesoma Ejikeme ta ci maki 362 wanda JAMB ta fito fili ta ƙaryata?

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: JAMB Ta Kammala Bincike Kan Mmesoma Ejikeme, Dalibar Da Ta Yi Karyar Cin Maki 362

Daga Karshe, Dalibar da Ake Zargi Da Maguɗin JAMB Ta Fadi Makin da Ta Ci Na Gaskiya

A ɗazu kun ji cewa Bayan lokaci ana kace nace, Ejikeme Mmesoma, ta aminta da cewa gaskiyar makin da ta ci a JAMB 2023 shi ne 249.

Hukumar JAMB mai alhakin shirya jarabawar shiga manyan makarantu UTME ta zargi ɗalibar 'yar jihar Anambra da buga sakamakon ƙarya har ta haramta mata jarabawa tsawon shekaru 3.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262