Daga Karshe, Dalibar da Ake Zargi Da Maguɗin JAMB Ta Fadi Makin da Ta Ci Na Gaskiya

Daga Karshe, Dalibar da Ake Zargi Da Maguɗin JAMB Ta Fadi Makin da Ta Ci Na Gaskiya

  • Bayan lokaci ana kace nace, Ejikeme Mmesoma, ta aminta da cewa gaskiyar makin da ta ci a JAMB 2023 shi ne 249
  • Hukumar JAMB ta zargi ɗalibar 'yar jihar Anambra da buga sakamakon ƙarya har ta haramta mata jarabawa tsawon shekaru 3
  • Amma ɗalibar ta yi bayanin cewa ko kaɗan ba laifinta bane domin tun asali JAMB ba ta aiko mata da sakamako ba bayan ta tura saƙo

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Anambra - Daga ƙarshe, Ejikeme Mmesoma, ɗalibar da ake zargin ta haɗa sakamakon jarabawar JAMB na karya, ta bayyana ainihin makin da ta ci na gaskiya.

Rahoton Daily Trust ya tattaro cewa ɗalibar ta amince da cewa maki 249 ta ci a jarabawar neman gurbin shiga manyan makarantun gaba da sakandire UTME 2023.

Rudani kan sakamakon jarabawar JAMB 2023.
Daga Karshe, Dalibar da Ake Zargi Da Maguɗin JAMB Ta Fadi Makin da Ta Ci Na Gaskiya Hoto: JAMB
Asali: Twitter

Idan baku manta ba hukumar shirya jarabawar wato JAMB ta zargi ɗalibar da haɗa sakamakon bogi wanda ya nuna cewa ta ci maki 362 cikin jumullar maki 400.

Kara karanta wannan

Jerin Muhimman Tambayoyin da Ya Zama Tilas JAMB Ta Amsa Kan Ɗalibar da Ake Zargi Da Ƙara Yawan Maki

Amma duk da haka, Mmesoma ta kafe kan bakarta cewa gaskiyar makin da ta samu kenan, lamarin da ya haddasa ruɗani da kace-nace tsakanin 'yan Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata sanarwa, kakakin JAMB na ƙasa, Dr. Fabian Benjamin, ya ce bayanai suna nuna ɗalibar ta tura sakonni zuwa na'urar sadarwar hukumar ciki harda sakamakon da ya nuna ta ci 362.

Bayan haka ne JAMB ta sanar da cewa ta haramta wa Mmesoma, ɗaliba daga jihar Anambra, zama jarabawar UTME na tsawon shekara uku, matakin ya bar baya da ƙura.

Menene gaskiya abinda ya faru?

Yayin hira a cikin shirin Sunrise Daily na Channels tv tare da mahaifinta ranar Laraba, Mmesoma, tace ba ita ya kamata a ɗora wa laifi ba dangane da wannan ruɗanin.

Mmesoma ta yi bayanin cewa ta tura saƙo kai tsaye zuwa JAMB ta sashin neman taimako amma shiru-shiru ba'a turo mata amsar sakamakon da ta ci ba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: JAMB Ta Kammala Bincike Kan Mmesoma Ejikeme, Dalibar Da Ta Yi Karyar Cin Maki 362

Ɗalibar ta ce:

"Saƙo ɗaya na tura musu, ba su turo mun amsa ba, idan suka duba na'urar taimako a JAMB zasu ga saƙon da na aika masu. Bayan duk abinda ya auku, yanzu na gano cewa 249 na ci."

JAMB Ta Kammala Bincike Kan Mmesoma Ejikeme

A wani labarin na daban kuma Hukumar JAMB ta bayyana cewa ta kammala bincike kan sakamakon bogi na ɗalibar Anambra, Ejikeme Mmesoma.

Ana zargin Mmesoma Ejikeme da ƙara yawan makinta na jarabawar 2023 UTME/JAMB, zargin da ta musanta duk da JAMB na ta bankaɗo hujjoji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262