Mawallafin Jaridar NewsDirect Dr Samuel Ibiyemi Ya Mutu

Mawallafin Jaridar NewsDirect Dr Samuel Ibiyemi Ya Mutu

  • An yi rashin mawallafin jaridar NewsDirect, Dr Samuel Ibiyemi wanda ya koma ga mahaliccinsa a ranar Talata, 4 ga watan Yuli
  • Samuel Ibiyemi ya mutu ne a asibitin koyarwa na jami'ar Babcock da ke jihar Ogun inda ya kwanta jinya
  • Gwamnan jihar ya aike da saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan mamacin wanda ya bayyana mutuwarsa a matsayin babban rashi a gare su

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ogun - Mawallafin jaridar News Direct, Dr Samuel Ibiyemi, ya mutu ya bar duniya.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa Ibiyemi ya mutu ne a ranar Talata da rana a asibitin koyarwa na jami'ar Babcock da ke a Ilishan Remo, jihar Ogun.

Dr Samuel Ibiyemi ya mutu
Marigayi Dr Samuel Ibiyemi Hoto: Newsdirect.com
Asali: UGC

Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya bayyana mutuwar Dr Samuel a matsayin wani babban abun takaici.

A cikin wani saƙon ta'aziyya da ya aike wa da iyalansa da abokan aikinsa, gwamna Abiodun ya bayyana Dr Ibiyemi a matsayin ɗan jarida mai hazaƙa wanda ya yi da amfani da ƙwarewarsa a aikin domin kawo ci gaba ga al'umma.

Kara karanta wannan

Magana Ta Ƙare: Shugaba Tinubu Ya Ɗora Nauyin Dawo da Zaman Lafiya A Zamfara Kan Mutum 1

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya bayyana cewa mamacin ya tsaya akan gaskiyarsa, inda ya yi nuni da cewa ta hanyar jaridarsa ya bayar da tasa gudunmawar wajen ci gaban tattalin arziƙi da siyasar Najeriya.

"Bai daɗe ba ya gano fannin kasuwanci na aikin jarida, hakan ya sanya ya fara wallafa. Ta hanyar jaridar NewsDirect, Dr Ibiyemi ya yi amfani da ƙwarewarsa da kuma zummar da yake da ita kan kasuwanci."
"Mutuwarsa babban rashi ne ga iyalansa da aikin jarida. Ya bar tarihi mai kyau wanda ba ya goguwa."

Wanene Dr Samuel Ibiyemi?

Ya yi digirinsa na farko a fannin tattalin arziƙi a jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ile Ife, ya yi digirin digirgir a fannin tattalin arziƙin man fetur a jami'ar jihar Legas, cewar rahoton Insidebusinesss.ng

Ibiyemi ya yi aiki a rundunar sojin sama inda daga nan ya tsunduma aikin jarida. Ya yi aiki da Financial Standard da Nigerian Tribune sannan daga baya ya kafa Nigeria NewsDirect. Shi ne kuma mamallakin otal ɗin Rejoice a jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Innalillahi: An shiga jimami a ABU, dalibin ajin karshe a likitanci ya kwanta dama

Dr Samuel Ibiyemi ya mutu ya bar matarsa Titilayo Ibiyemi, babbar jami'ar ɗan sanda da ƴaƴa.

Babban Fasto Ya Bar Duniya

A wani labarin na daban kuma, wani babban fasto a cocin The Evening da ke a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom, Fasto Runcie Mike, ya mutu.

Babban faston ya yi bankwana da duniya ne kwana ɗaya bayan ya jagoranci bikin binne wata gawa a cocin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng