Dalibin Jami'ar UMYU Da Ke Wankin Mota Ya Bayyana Dalilinsa Na Yin Sana'ar
- Dalibin jami'ar Umaru Musa Yar'adua (UMYU), da ke Katsina ya zaɓi ya kamata sana'ar wankin mota don ɗaukar dawainiyar karatunsa
- Dalibin mai Suna Sani Usman, ya kuma bayyana cewa sana'ar da ita ya dogara wajen yin sauran kwaranniyoyinsa na rayuwa
- Ya ce ya zaɓi ya fara sana'ar ne domin ya samu damar dogaro da kansa ba tare da ya ci gaba da ɗorawa iyayensa nauyi ba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Katsina - Dalibin jami'ar Umaru Musa Yar'adua (UMYU), mai suna Sani Usman, ya bayyana cewa ya zaɓi ya kama sana'ar wankin mota ne saboda ya dogara da kansa.
Matashin a hirarsa da sashen Hausa na rediyon DW, ya bayyana cewa iyayensa ba masu ƙarfi ba ne.
Dalibin ya ce baya son ɗorawa iyayensa ƙarin nauyi
Ya ce ya duba ne ya ga cewa bai kamata ya zauna haka nan ba tare da yin wani abu da zai riƙa samun kuɗaɗe ba, domin gudun kar ya ƙara ɗorawa iyayensa nauyi.
"Ba Zan Amsa Ba Sai Kin Duƙa Kan Guiwa" Bidiyon Yadda Wani Magidanci Ya Ƙi Karban Abinci Daga Matarsa Ya Ja Hankali
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Matshi Sani Usman dai na gudanar da sana'arsa ta wankin motocin ne a babbar tashar motar nan ta NATO, wacce ke cikin birnin Katsina.
Sani yaa bayyana cewa da wannan sana'a ta wankin mota da yake yi ce ya ɗauki nauyin ƙarantunsa na NCE da ya yi.
A kalamansa:
“Bayan na kammala ban samu aikin yi ba sai na ga ya kamata na faɗaɗa karatuna, shi ne sai na tafi jami'ar Umaru Musa Yar'adua da ke nan Katsina, inda a yanzu haka ina aji uku ina karatun digiri.”
Ɗalibin ya ce baya jin kunyar sana'ar wankin motar da yake yi
Ya kuma ce ko kaɗan baya jin kunyar sana'ar wankin motar da yake yi, domin ko a cewarsa rashin sana'a ne abin kunya.
a cewarsa:
“Abin kunya a wurin ɗa na miji, shi ne a ce ya zauna bai da sana'ar da yake yi, duba da mun taso 'ya'yan talakawa, idan muka zauna ba mu aikin komai, zamu ƙara ɗorawa iyayenmu nauyi.”
Da yake tsokaci game da ɗalibin, Dakta Kabir Umar Musa, wanda malami ne a jami'ar UMYU, ya shawarci matasa su yi koyi da irin ɗabiun matashi Sani Usman.
Ya ce ba dole ba ne sai iyayen mutum suna da kuɗi ko kuma suna da rai ne kawai zai iya yin karatu ba. Ya ce muddun kana da sana'ar da kake samun taro da sisi, zaka iya ɗaukar nauyin karatunka.
Malamin ya ƙara da cewa yin karantun zai taimakawa mutum a gaba kan kowace iriyar sana'a ce ya zaɓi ya yi, wanda rashinsa ka iya kawo ci baya a wajen gudanar da sana'ar.
Kungiyar ASUU ta fusata da matakin Tinubu kan shugabannin majalissun jami'o'i
Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan martanin da kungiyar malaman jami'a ta kasa (ASUU), dangane da sauke shugabannin majalisun dake sanya idanu kan harkokin jami'o'in Najeriya.
ASUU ta ce wannan mataki da Shugaba Bola Tinubu ya dauka zai kawo cikas a al'amura da dama na jami'o'in Najeriya.
Asali: Legit.ng