Daga Shafin JAMB Na Cire Sakamkon Jarabawa Ta, Dalibar Anambra Ta Maida Martani

Daga Shafin JAMB Na Cire Sakamkon Jarabawa Ta, Dalibar Anambra Ta Maida Martani

  • Ɗalibar da tafi sauran dalibai cin makin jarabawa JAMB, Ejikeme Mmesoma, ta ce ko kaɗan bata kirkiri sakamakon bogi ba
  • Hukumar JAMB ta yi zargin cewa ɗalibar yar asalin juhar Anambra ba maki 362 ta ci ba, asalin makin da ta samu shi ne 249
  • Amma a martanin da ta yi yau Litinin, ta ce bata san ya ake kara wa maki ba kuma a tunaninsa akwai inda aka samu matsala

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ɗalibar makarantar sakandiren mata ta Anglican da ke Nnewi, Anambra, Ejikeme Mmesoma, ta maida martani kan zargin da ake mata na ƙara yawan makin da ta ci a jarabawar share fagen shiga manyan makarantu UTME.

Bisa makin da ta wallafa cewa ta samu a jarabawar bana 362, an bayyyana ɗalibar a matsayin wacce ta fi kowa yawan maki kuma ta samu kyaututtuka da dama kan haka.

Kara karanta wannan

Manyan gobe: JAMB ta tona asirin dalibar ta yi karyar cin maki 362, aka bata kyautar N3m

Ejikeme Mmesoma.
Daga Shafin JAMB Na Cire Sakamkon Jarabawa Ta, Dalibar Anambra Ta Maida Martani Hoto: dailytrust
Asali: UGC

JAMB ta ce sakamakon ƙarya ne

A wata sanarwa da kakakin hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu JAMB, Fabian Benjamin, ya fitar ranar Lahadi ya ce ɗalibar ta ci maki 249 ne ba 362 da take yaɗawa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Benjamin ya bayyana cewa ɗalibar ta jirkita sakamakon jarabawar da ta zana ne don kawai ta samu kyaututtuka kuma ta ja hankali, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Ya ce hukumar JAMB zata kwace sakamakon yayin da ɗalibar, Mmesoma zata fuskanci hukunci daidai da abinda ta aikata.

Ɗalibar ta maida martani

Amma da take maida martani ranar Litinin, ɗalibar ta bayyana cewa a shafin hukumar JAMB ta duba sakamakon jarabawar. A cewarta ba ta san yadda ake buga sakamakon bogi ba.

Ta ce tun da take a rayuwarta ta kasance ɗaliba mai hazaka da basira kuma tun tana makarantar Firamare take cin na ɗaya, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Babban Lauya Ya Bayyana Mataki Na Gaba da Ya Kamata Tinubu Ya Ɗauka Kan Bawa da Godwin Emefiele

Mmesoma ta ce 'yan sanda sun gayyace ta Caji Ofis kuma sun ɗauki bayananta, sannan sun faɗa mata cewa ana kan bincike kan wannan rikita-rikita.

A cewarta, abinda ya faru ya yi matuƙar gigita ta kuma tana zargin, "Tabbas akwai inda matsalar take."

Tsohon Ministan Birnin Tarayya Abuja Ya Mutu, Bayanai Sun Fito

A wani labarin na daban kuma Ministan babban birnin tarayya Abuja na farko bayan an kafa ta a 1976, Chief Mabolaji Ajose-Adeogun, ya riga mu gidan gaskiya.

Mamban iyalan gidan marigayin, Oluremi Ajose-Adeogun, ya ce tsohon ministan ya rasu ne ranar Asabar 1 ga watan Yuni, 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262