An Shiga Jimami Bayan Babban Malamin Addini Ya Koma Ga Mahaliccinsa Kwana 1 Bayan Ya Jagoranci Binne Gawa

An Shiga Jimami Bayan Babban Malamin Addini Ya Koma Ga Mahaliccinsa Kwana 1 Bayan Ya Jagoranci Binne Gawa

  • Wani babban fasto na cocin The Evening Church, a Uyo, jihar Akwa Ibom, Fasto Runcie Mike, ya bar duniya
  • Shugabannin cocin sun bayyana a cikin wata sanarwa cewa Fasto Mike ya mutu ne bayan ya yi fama da ƴar gajeruwar rashin lafiya a ranar Asabar, 1 ga watan Yuli
  • Mambobin cocin da abokanai sun yi magana kan mutuwar faston wanda ya jagoranci binne wata gawa a ranar Juma'a

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Uyo, jihar Akwa Ibom - An shiga jimami a ranar Asabar biyo bayan mutuwar Fasto Pastor Runcie Mike, babban faston cocin The Evening Church a Uyo, jihar Akwa Ibom, bayan ƴar gajeruwar rashin lafiya.

A cewar shugabannin cocin, Fasto Mike ya mutu ne a ranar Asabar, 1 ga watan Yuli, kwana ɗaya bayan ya jagoranci binne wata gawa a ranar Juma'a, PM News ta rahoto.

Kara karanta wannan

Abun Bakin Ciki: Yan Bindiga Sun Kashe Faston RCCG, Sun Sace Mutum 7 Ana Tsaka Da Bauta

Fasto Runcie Mike ya mutu a ranar Asabar
Fasto Runcie Mike ya mutu kwana daya bayan ya jagoranci bikin binne gawa Hoto: Pastor Runcie Mike
Asali: Facebook

Shugabannin cocin sun bayyana cewa:

"A wannan lokaci na jimami, muna roƙon al'umma da su sanya mu a cikin addu'o'insu musamman iyalansa na kusa da shi."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mambobin cocin da abokai sun yi magana biyo bayan mutuwar Fasto Runcie Mike

Mambobin cocin da abokanan Faston sun nuna jimaminsu da takaicinsu kan mutuwar Faston a Soshiyal Midiya.

Wata mai suna Debbie Iteh, wacce ta sanya bidiyon Faston a wajen bikin binne wata gawa a ranar Juma'a ta rubuta cewa:

"Ban taɓa ganin Fasto Mike yana kuka irin haka ba a wajen bikin binne gawar ɗaya daga cikin mambobin cocinsa a ranar Juma'a."
"Lokacin da na ga bidiyon nan, na ji cewa mutumin nan akwai abinda yake damunsa a lokacin wanda ya sosa masa zuciya, yanzu ga shi labarin mutuwarsa ya karaɗe soshiyal midiya. Mutumin da ya jagoranci binne gawa shi ne yanzu ya mutu?"

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Bayan An yi Rashin Wani Babban Likita a Arewacin Najeriya

Wani mamban cocin, Eunice Obed Ufford ya rubuta:

"Tun karfe 2:00 na dare idanu na ke a buɗe ina ta kallon taga, na duba sama na tsunduma duniyar tunani."

A nasa ɓangaren Gospel Edoho, ya rubuta:

"Abun baƙin ciki da jimami. Hawaye sun cika min ido yanzu. Fasto Runcie Mike ya amince ya zo cocinmu sati mai zuwa bai tare da an ba shi ko sisi ba"

An Yi Rashin Babban Basarake

A wani labarin kuma, an shiga jimami biyo bayan rasuwar wani babban basarake a jihar Ogun, wanda ya yi bankwana da duniya.

Babban basaraken jihar Ogun, Oba Saburee Babajide Isola Bakre, Jamolu II na Gbagura, Egbaland, a Abeokuta, ya riga mu gidan gaskiya, bayan ya yi ƴar gajeruwar jinya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng