Bayan Kwanaki Uku Da Haduwa, Matashi Ya Rabu Da Sabuwar Budurwarsa Saboda Rashin Kwarewa a Rubutu

Bayan Kwanaki Uku Da Haduwa, Matashi Ya Rabu Da Sabuwar Budurwarsa Saboda Rashin Kwarewa a Rubutu

  • Wani mai amfani da Facebook ya rabu da sabuwar budurwarsa saboda rashin kwarewa a bangaren rubutu
  • Wallafarsa ya tayar da kura a soshiyal midiya yayin da aka yi muhawara kan muhimmancin iya rubutu a soyayya
  • Bai bayyana sunan budurwar ba da kuma ko ya tuntube ta tun bayan wallafar tasa

Wani mai amfani da Facebook ya yanke shawarar kawo karshen soyayyarsu da wata budurwa da ya hadu da ita a soshiyal midiya saboda rashin kwarewarta a bangaren rubutu.

Ya nuna bacin ransa a cikin wani rubutu da ya yi a Facebook wanda ya yadu.

Matashi cikin damuwa
Bayan Kwanaki Uku Da Haduwa, Matashi Ya Rabu Da Sabuwar Budurwarsa Saboda Rashin Kwarewa a Rubutu Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Wani bangare na rubutunsa na cewa:

"Hirar kwanaki uku sannan bata yi amfani da wa'kafi, ko alamar tambaya ba! Cewa kawai take yi "Ka ci abinci". Menene wannan? Tambayata kike yi ko kina fada mani wani abu ne? Shin na nemi abu da yawa?"

Kara karanta wannan

“Kamar a Fim”: Matashiya Ta Auri Hadadden Dan Koriya a Asiya, Hadadden Bidiyon Bikin Ya Zautar Da Yan Mata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Saurayi ya gaza jure rashin iya nahawu daga budurwarsa

Itodo, wanda ya kasance malamin makaranta ya ce ba zai iya jurewa ba ace budurwarsa bata da kwarewa a bangaren nahawu da rubutu.

Rubutun nasa ya haifar da dubban martani daga masu amfani da TikTok.

Wasu daga cikinsu sun marawa shawarar da ya yanke baya sannan sun ce suna matukar mutunta kwarewar rubutu tattare da masoyansu.

Sauran mutane sun ce kwarewar rubutu ba wani abu bane kuma cewa ya kamata ya mayar da hankali a al’amuran da suka shafi halin budurwarsa.

Sai dai kuma, wasu sun ce kwarewar rubutu bai da muhimmanci a Najeriya cewa mutane na da abubuwan da suka fi damunsu wanda za su magance.

Sun ce kwarewar rubutu bai da muhimmanci wajen hirar yau da kullun sannan cewa mutane na iya fahimtar junansu ba tare da shi ba.

Kara karanta wannan

An kuma: Za a saka wa 'yan Twitter takunkumi, an fadi adadin rubutun da za su ke gani a rana

Jama'a sun yi martani

Oluwa Rhoda ta rubuta:

"Baka nemi abu da yawa ba fa."

Aninath Okpongete ta yi martani:

"Ka ci gyaranta cikin mutunci, ka yi amfani da kalamai masu taushi, ka bari ta sani cewa babban abu ne a gareka. Idan har ka damu da soyayyar kenan."

Vee Vian ta yi martani:

"Wannan ya zautar dani sosai...Kawai na bar maka tattaunawar nan, kafin na cire gashin da ke kai....Kawai ka sanya alamar tambaya, idan ka yi tambaya."

Matashiya ta auri hadadden saurayi dan Koriya, hotuna da bidiyonsu sun yadu

A wani labari na daban, wata kyakkyawar budurwa yar Afrika ta angwance da hadadden saurayinta dan kasar Koriya.

Hotuna da bidiyoyin masoyan ya matukar daukar hankalin jama'a a soshiyal midiya yayin da yan mata suka mato a kansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng