Shugaba Bola Tinubu Ya Ziyarci Oba Na Legas, Ya Kai Masa Babbar Gaskiyar Ban Girma
- Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu a gana da Oba na Legas a fadarsa da ke a jihar ta Legas a Kudu maso Yamma
- Wannan na zuwa ne bayan ya gana da shugaban kasar Guinea Bissau Umaro Embalo a gidansa da ke Legas
- Tinubu ya tafi hutun sallah jiharsa jim kadan bayan da ya dawo daga kasar Landan a wata ziyara da ya kai
Jihar Legas - A ranar Asabar ne shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyarar ban girma ga Oba na Legas, Rilwan Aremu Akiolu, a fadarsa, Channels Tv ta ruwaito.
Hakan ya biyo bayan ziyarar aiki da shugaban kasar Guinea Bissau Umaro Sissoco Embaló ya kai wa Tinubu a gidansa da ke Ikoyi, Legas.
Ziyarar Tinubu zuwa Oba na Legas kuwa, na iya zama ba sabon abu ba, idan aka yi la’akari da dangantakar kud-da-kud da mutanen biyu suka dade da ita.
Tinubu dai dan asalin jihar Legas ne, kuma ya yi gwamna shekaru takwas a jihar, inda ake masa ganin wanda ya saura zubin jihar zuwa yadda take a zamanance a yanzu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kafin zuwansa ga Oba, ya gana da shugaban Guinea Bissau
Mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan ayyuka na musamman, sadarwa, da dabaru, Dele Alake, ya shaidawa manema labarai cewa, duk da cewa Embaló ya kawo ziyarar ce ta sirri, ya zo ne domin nuna goyon bayansa ga shugaban Najeriya.
A wani bidiyon da gidan talabijin din kasa na NTA ya yada, an ga lokacin da Tinubu ke tarbar shugaban kasar tare da wasu manyan jiga-jigai na kasar nan.
Kuma, ita ce ziyara ta farko da wani shugaba na Afrika ya taba kawo wa Tinubu tun bayan da ya karbi mulki a ranar 29 ga watan Mayun da ta gabata.
Shin da gaske ne za a kara wa Tinubu da Shettima albashi?
A wani labarin, an bayyana yadda wani rahoto ke yawo cewa, za a kara albashi ga Tinubu da kuma sauran manyan gwamnati.
Tuni dai bincike ya gano ba haka bane, inda aka fayyace yadda gaskiyar batun yake tun daga tushe.
An kuma bayyana shirin da gwamnati ke yi na karin albashin da kuma inda maganar ta kwana.
Asali: Legit.ng