“Ya Koma Waje Mai Nisa Sosai” Hadimin Buhari Ya Magantu Kan Sabon Wurin Da Tsohon Shugaban Kasar Ya Koma
- Tsohon shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya bar mahaifarsa ta Daura, jihar Katsina, makonni bayan ya koma gida
- Kakakin Buhari, Garba Shehu, ya ce tsohon shugaban kasar ya bar Daura saboda baki na yawan damunsa
- Shehu ya ce Buhari ya bar kasar ne don gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta samu kyakkyawar yanayi na yin aiki
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Tsohon kakakin tsohon shugaban kasa Garba Shehu ya ce tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar mahaifarsa da ke Daura, jihar Katsina.
Shehu ya yi bayanin cewa Buhari ya bar Daura zuwa wata uwa duniya saboda ya gaza samun shirun da yake son samu bayan barin mulki a ranar 29 ga watan Mayu, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Sai dai kuma, bai bayyana sabon wurin da Buhari ya koma ba.
Dalilin da yasa Buhari ya bar mahaifarsa a Daura
Shehu, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, 29 ga watan Yuni, yana mai cewa Buhari ya bar Daura saboda "baki da ke yi masa zarya safe, rana da dare."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar The Nation, ya ci gaba da bayyana cewa Buhari ya so samar da yanayi da gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu za ta yi aiki.
Ya ce:
"Ya zabi komawa gida a Daura, yana mai fatan samun irin yanayin da yake sowa kansa na rashin hayaniya amma sai ya gane cewa wannan ba shine abun da ya faru ba, baki na ta zarya safe, rana da dare, ya tafi wani wuri mai nisa.
"Wannan shine fatansa cewa a barsa ya samu isasshen hutun da yake bukata da kuma ba gwmanatin Tinubu yanayin da ya dace domin aiki kan cimma alkawaran da suka dauka."
Shehu Sani ya nemi Tinubu ya binciki gwamnatin Buhari
A wani labarin, Sanata Shehu Sani ya bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya ci gaba da binciken jami'an gwamnatin baya ta Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Sani ya ce dole shugaban kasar ya kwato kudaden da barayin gwamnati suka wawure a kasar nan domin idan bai aikata haka ba toh ko ba jima ko ba dade kudaden da aka wawure za su yo farautarsa da kansu.
Asali: Legit.ng