Sojoji Sun Kama Masu Sace Karafunan Titin Jirgin Kasa a Nasarawa, Ta Ki Karbar Cin Hancin Miliyan N5

Sojoji Sun Kama Masu Sace Karafunan Titin Jirgin Kasa a Nasarawa, Ta Ki Karbar Cin Hancin Miliyan N5

  • Dakarun rundunar sojojin Najeriya a shiyar Doma, jihar Nasarawa, sun kama wasu da ake zargin masu satar karafunan jirgin kasa ne
  • A cewar kakakin rundunar, Manjo Joseph Afolasade, akalla mutane 12 aka kama kuma sun fadi wasu zantuka
  • An tattaro cewa mutanen da aka kama sun yi kokari ba dakarun sojin cin hancin naira miliyan 5, wanda suka ki karba

Nasarawa, Angwan Yara - Dakarun rundunar sojojin Najeriya a Doma, jihar Nasarawa sun ki karbar cin hancin naira miliyan 5 da wasu masu satar karafunan jirgin kasa suka basu a Angwan Yara, karamar hukumar Keana ta jihar.

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, an kama masu satar karafunan kuma yanzu haka suna tsare a hannun rundunar sojojin Najeriya.

Dakarun rundunar sojojin Najeriya
Sojoji Sun Kama Masu Sace Karafunan Titin Jirgin Kasa a Nasarawa, Ta Ki Karbar Cin Hancin Miliyan N5 Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Mukaddashin kakakin rundunar sojoji na shiyar Doma, Manjo Joseph Afolasade ne ya tabbatar da ci gaban yayin wani taron manema labarai a ranar Juma'a, 30 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu Ta Kirkiro Sabuwar Hanyar Tatsar Kudi Daga Masu Hawa Titi

Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A ranar 15 ga watan Yuni, dakarun rundunar, yayin wani aikin fatrol sun kama wasu masu sace karafunan titin n jirgin kasa a wani titin jirgi da baya aiki tsakanin Angwan Yara da Agyaragu na karamar hukumar Keana.
"An kama mutanen da karafunan titin jirgin kasa masu yawa da aka loda a cikin manyan motoci biyu."

A cewar jaridar Vanguard, kakakin rundunar ya bayyana cewa an kama wasu daga cikin wadanda ake zargin a ranar Lahadi, 18 ga watan Yuni.

Ya bayyana cewa a yayin yi masu tambayoyi, duk sun fallasa wasu sirrika sannan sun yarda cewa suna sace karafunan titin jiragen kasa.

An tattaro cewa sun bayyana sunayen wadanda suka hada baki da su wadanda aka ce fitattun mutane ne a jihohin Nasarawa da Filato.

Kakakin rundunar ya ce:

"Sun yarda da taka rawar gani wajen sace-sacen karafunan titin jirgin kasa sannan sun ambaci sunayen wasu manyan mutane a jihohin Narawa da Filato cikin yan kungiyar."

Kara karanta wannan

Shari'ar Tinubu, Atiku Da Obi: Fitaccen Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Sha Kakkausar Suka Daga 'Yan Najeriya Kan Hasashen Da Ya Yi

Yadda dakarun sojoji suka ki amsar cin hancin miliyan N5 daga wadanda ake zargin

Kakakin rundunar ya bayyana cewa wadanda ake zargin sun yi wa dakarun rundunar tayin naira miliyan 5 a matsayin cin hanci amma suka ki karba.

Ya bayyana cewa an gaggaunta kama wadanda ake zargin kuma za a mika su ga hukumar NSCDC domin gudanar da bincike da kuma hukunta su.

Daya daga cikin wadanda ake zargin, Hasiru Modibbo, ya fada ma manema labarai cewa daya daga cikin abokan kasuwancinsa ya kira shi daga baya inda aka aika N300,000 ga direbobin manyan motocin biyu.

An nemi mataimakin shugaban kungiyar MACBAN na kasa an rasa

A wani labari na daban, kungiyar Miyetti Allah ta koka kan batan mataimakin shugabanta na kasa, njiniya Munnir Atiku Lamido.

An nemi Lamido an rasa ne bayan ya bar gidansa da ke jihar Katsine inda ya tafi wani taro a jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng