Tsohon Gwamnan Rikon Kwarya a Jihar Bayelsa, Nestor Binano, Ya Mutu

Tsohon Gwamnan Rikon Kwarya a Jihar Bayelsa, Nestor Binano, Ya Mutu

  • Jihar Bayelsa ta rasa tsohon gwamnan rikon kwarya, Honorabul Nestor Binabo, wanda ya mutu ranar 29 ga watan Yuni, 2023
  • Da yake martani kan wannan rashi, gwamna Douye Diri ya ce Binabo ginshiƙi ne da ya bada gudummuwa wajen bunƙasa jihar Bayelsa
  • A sakon ta'aziyyar da ya aike wa iyalai da sauran mutanen jiha, Diri ya jaddada cewa za'a yi kewar Binabo a fagen siyasa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Bayelsa State - Tsohon gwamnan riƙon kwarya a jihar Bayelsa, Honorabul Nestor Binabo, ya riga mu gidan gaskiya, kamar yadda jaridar This Day ta ruwaito.

Marigayi BinaAbo ya mutu ne ranar Alhamis, 29 ga watan Yuni, 2023 a wani asibiti a birnin tarayya Abuja bayan fama da rashin lafiya.

Gwamna Douye Diri da marigayi Binabo.
Tsohon Gwamnan Rikon Kwarya a Jihar Bayelsa, Nestor Binano, Ya Mutu Hoto: Douye Diri, Bayelsa State Government
Asali: Facebook

Honorabul Binabo ya yi aiki a matsayin gwamnan rikon kwarya na jihar Bayelsa na ɗan taƙaitaccen lokaci tsakanin 27 ga watan Janairu zuwa 14 ga watan Fabrairu 2012.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Fitaccen Farfesan Najeriya Ya Rasu a Bauchi

Gwamna Diri ya yi ta'aziyyar rasuwar Binabo

A saƙon ta'aziyyan da ya aike wa al'ummar Bayelsa da iyalan mamacin, Gwamna Douye Diri, ya ce Binabo ɗan siyasa ne na asali kuma za'a yi matuƙar kewarsa a fagen siyasar jiha.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce marigayi Binabo ya ba da gudummuwa gagara misali wajen kawo ci gaba a jihar Bayelsa amma ya tafi ya barmu a daidai lokacin da Allah ya zaɓa duk da faman jinyar da ya yi.

Wannan saƙo na kunshe a wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamna Diri, Mista Daniel Albrah ya fitar, kamar yadda rahoton Tribune online ya tabbatar.

A cikin sanarwan an ji gwamna Diri na cewa:

"Ina addu'a Allah ya bai wa iyalansa hakuri da juriyar wannan babban rashi da suka yi."

Ɗan a mutun Atiku, Idi Amin, ya rasu

Kara karanta wannan

Masu Yaɗa Jita-Jitar Gwamnan APC Ya Mutu Sun Shiga Uku, Gaskiya Ta Yi Halinta

Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Alhaji Idrissu Amin, wanda aka fi sani da Idi Amin, mamban kwamitin kamfen shugaban kasa na PDP, ya kwanta dama.

Idi Amin, ɗan siyasa kuma na kusa da Atiku Abubakar, tsohon ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, ya cika ne a birnin tarayya Abuja.

Zamu Kama Duk Mai Yada Jita-Jitar Gwamna Akeredolu Ya Mutu, Jam'iyyar APC

A wani rahoton na daban kuma APC ta bayyana cewa ta shiga damuwa sakamakon jita-jitar da ake yaɗawa cewa gwamnan Ondo ya mutu.

Shugaban APC na jiha ya ce masu yaɗa labarin na ƙarya ba su da aikin yi, kuma duk wanda ya shiga hannu zai gane kurensa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: