Gwamnatin Tinubu Ta Kirkiro Sabuwar Hanyar Tatsar Kudi Daga Masu Hawa Titi
- Daga watan Yulin 2023, Gwamnatin tarayya za ta rika karbar kudi domin bada takardar shaidar POC
- Duk wani mai abin hawa zai rika biyan N1000 a kowace shekara da nufin ya mallaki wannan satifiket
- Za a rika tatsar masu motoci, babur da tireloli kafin su samu takardar da ke nuna mallakar abin hawansu
Abuja - Gwamnatin tarayya za ta fara bada takardar shaidar POC mai nuna mallaka ga masu kowane irin abin hawa a jihohin da ke fadin Najeriya.
Babban sakataren ma’aikatar sufuri na gwamnatin Legas, AbdulHafiz Toriola ya yi bayanin shigowar wannan tsari, The Nation ta fitar da labarin.
Injiniya AbdulHafiz Toriola ya nuna satifiket din zai fito ne a watan Yulin nan da za a shiga.
Da yake bayani a kan tsarin a cibiyar yada labarai ta Bagauda Kaltho da ke Alausa a Legas, Toriola ya ce wajibi ne masu abubuwan hawa su mallaki POC.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tsari ya canza a Najeriya
Jami’in gwamnatin ya kuma ce duk shekara sai an biya kudi domin sabunta wannan satifiket, a maimakon a rika biya idan an saye gwanjon abin hawa.
A baya ana biyan wannan kudi ne idan aka saye mota ko babur, ko kuwa aka canza masa inji.
Wannan satifiket zai zama cikin takardun da ake bukata a samu daga duk wani mai tirela, tifa, gingimari, karamar mota, keke napep, babur da sauransu.
Jaridar ta rahoto Toriola ya na cewa POC zai kunshi bayanin mutum da su ka hada da lambar abin hawa, shekarar kira, baya ga sunansa da adireshinsa.
Za a fara karbar N1000 a jihohi
Ana sa ran jihohin kasar nan su fara dabbaka wannan shiri daga Yuli. Abin da mutum zai biya domin samun satifiket shi ne akalla N1, 000 a shekara.
Rahoton Premium Times ya ce gwamnatin Legas ta fara dabbaka wannan tsari kamar yadda doka tayi tanadi domin inganta tsaro da tabbatar da gaskiya.
Gwamnati ta ce batun bada shaidar mallakar abin hawa ya na cikin sashe na 73- (1) mai lamba 101 na amfani da titi da ya wajabta yi wa abin hawa rajista.
Rayuwa ta kara wahala a yau
Kun samu labari cewa samun ilmi ya na neman zama sai wane da wane, kudin karatu a wasu jami'o'i ya nunku kafin a murmure daga tsadar fetur.
Kudin dakin kwanan dalibai kawai ya koma tsakanin N37, 590 zuwa N80, 090 a Jami’ar BUK. Yanzu sai dalibi ya kashe akalla N97, 000 duk shekara.
Asali: Legit.ng