Babbar Sallah: Bayani, Sharuda da Ka’idojin da Ya Kamata Duk Mai Layyah Ya Kiyaye
- Sheikh Kabir Asgar ya yi wani rubutu mai dauke da bayani a kan layya da Musulmai za su yi
- Taƙaitaccen bayanin malamin ya tabo hukunci, dabbobi, sharuda da kuma ka’idoji wannan ibada a addini
- Asgar malamin musulunci ne kuma kwararren malamin larabci mai karantarwa a jami’ar ABU Zariya
A wani rubutunsa a Facebook, Kabir Asgar ya yi bayani a kan abin da ya shafi layyah.
Layya wajibi ce ga duk wanda ke da hali. Dabba guda ɗaya ta wadatar ga mai gida da iyalinsa, idan kuma an sami ƙari to ya yi kyau. Ko da kuwa zai kai ga kowane mutum guda a ba shi dabbarsa.
Lokacin yanka dabbar layya yana farawa ne daga sa’adda limamin idi ya yanka dabbarsa a ranar sallar har zuwa faduwar ranar 13 ga watan Zhul Hijja.
Zubar da jinin shine abin da shari'a ta ke so, don haka ba daidai ba ne a yi sadaka da kuɗin dabbar a maimakon yankawa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Malamai sun ba da fatwa akan halascin yanka dabba bayan wucewar lokacin (ga wanda ke da uzuri karɓaɓɓe kamar wanda dabbarsa ta ɓata sai ya ganta bayan lokacin).
SHARUƊƊAN DABBAR LAYYA
I. Dole dabba ta zama daga cikin dabbobin ni’ima (Raƙuma, Shanu, Tumaki da Awaki).
II. Dole ne dabbar ta zama ta kai shekarar da sharia ta gindaya (Raƙumi shekara 5, Shanu shekara 2, Tumaki da awaki shekara 1).
III. Dole ne dabbar ta zama ta kuɓuta daga aibi ko naƙasa mabayyaniya (kamar makanta, karyewa, gurguntaka, rama mai tsanani, rashin lafiya da sauransu).
IV. Dole ya zama mutumin da zai yanka dabbar ya mallake ta ne ta hanya karɓaɓɓiya a Shari'a (ba a yin layya da dabbar sata, ko ta kwace, ko ta aro, ko ta jingina ko wadda ake da tarayya a kan mallakarta).
Abubuwan da ya kamata a kiyaye
An so mutum ya yanka dabbar sa da kansa idan zai iya
Addu’ar da ake yi wajen yanka ita ce: (بسم الله اللهم تقبل منا)
Ana son a sami wuƙa mai kaifi don gujewa wahalar da dabba.
Wace dabba ta fi?
Akwai fifiko na jinsi
Akwai kuma na siffa
Dangane da jinsi an fi son
- Raƙumi
- Sannan shanu
- Sannan Tumaki
- Sannan Awaki
- Sannan tarayya akan Raqumi (mutum bakwai)
- Sannan tarayya akan Saniya (mutum bakwai)
Dangane da siffa ana son
- Mai kiba
- Mai tsadar farashi
- Mai kyaun siffa
- Mai koshin nama
- Da dai sauran siffofi na kamala
Ya ake yin rabon naman layya?
- Babu laifi a ci a gida
- Sannan a yi kyauta
- Da sadar da zumunci
- Da sadaka
- Sannan a taskace
- An so a fifita bai wa mabuƙata (talakawa, marayu, zawarawa, baƙi da sauran masu ƙaramin samu).
Karin bayani game da layyah
- Ba mustahabbi ba ne mutum ya yi aski bayan ya yanka layyarsa.
- Idan mutum ya sai dabba da niyyar layya bai halasta ya sai da ta ko da da nufin canzawa ne ba sai dai in zai sayar ne ga wani wanda shima layyar zai yi ko kuma ya kyautar ga mai yin Layya.
- Matafiyi na yin layya kamar yadda mazaunin gida ke yi.
- Wakilin maraya yana da damar ya yi masa layya a cikin dukiyarsa bisa ma’arufi.
- Ya halasta mutum ya ci bashin kudin da zai sayi dabba ko ya ci bashin dabbar layya.
- Hakanan kuma ya halasta ga wanda ake bin sa bashi ya jinkirta biyan bashin domin ya saye dabbar layya. Amma ba daidai bane ya yi roƙo ko barar dabbar layya ba.
- Idan aka bai wa mutum kyautar dabbar layya yana da cikakken tasaruffi a kan dabbar don ta zama dukiyarsa.
- Layya na cikin ciyarwa, don haka mace na iya yin layya da dukiyar mijinta ga iyalansa ko ba da izini ko saninsa ba.
- Idan layya ta hadu da aƙiƙar raɗin sunan jariri kuma guda ɗaya ake da halin yi. To ana gabatar da wacce ta fara zuwa ne in ba rana daya suka zo ba. In kuwa rana daya suka zo to sai a yi aƙiƙa.
- Ana yi wa mamaci layya idan ya yi wasiyyar a yi masa layya a cikin ɗaya bisa ukun dukiya. Haka kuma mutumin da ya sayi dabba sai Allah ya yi masa rasuwa kafin yanka dabbar za a yanka ta ranar sallah.
Sokoto: An Yi Jana'izar Mahaucin da Jama'a Suka Kashe Bisa Zargin Ɓatanci Ga Annabi SAW, Shaidu Sun Bayyana Gaskiya
Babu hawan sallah a Minna
Mai martaba Sarkin Minna, Alhaji Umar Farouk Bahago ya fasa yin hawan sallah, ya fadi rashin tsaro a matsayin dalilin da ya jawo ba za a shirya hawan ba.
A ‘yan shekarun bayan nan, an ji labari cewa an gagara yin hawan sallah a wasu garuruwa kamar Daura da Katsina saboda ta’adin ‘yan bindiga a yankin.
Asali: Legit.ng