Kisan Mutum 32: Al’ummar Hausawan Taraba Sun Nemi a Kwato Masu Hakkinsu

Kisan Mutum 32: Al’ummar Hausawan Taraba Sun Nemi a Kwato Masu Hakkinsu

  • Hausawa a karamar hukumar Takum ta jihar Taraba sun koka kan kisan gillar da ake yi wa al'ummarsu
  • Kakakin al'ummar Hausa a yankin, Alhaji Sani Abdullahi Tullu, ya yi kira ga gwamnatin jihar Taraba da ta gaggauta daukar mataki kan kashe masu muten 32 da aka yi
  • Ana dai zargin mayakan kabilar Kuteb da yawan kaiwa al'ummar hare-hare ba tare da dalili ba

Taraba - Al'ummar Hausawa a karamar hukumar Takum ta jihar Taraba sun bukaci a kwato masu hakkinsu kan kisan mutanensu 32 da ake zargin mayakan Kuteb sun yi.

Da yake jawabi ga manema labarai a Jalingo a ranar Lahadi, 26 ga watan Yuni, mai magana da yawun al'ummar, Alhaji Sani Abdullahi Tullu, ya kira ga gudanar da bincike a kashe-kashen, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Babban Dan Kwankwasiyya Ya Soki Rusau Da Abba Gida Gida Ke Yi A Kano, Ya Ce Ba Daidai Ba Ne

Gwamnan jihar Taraba
Kisan Mutum 32: Al’ummar Hausawan Taraba Sun Nemi a Kwato Masu Hakkinsu Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Ya bukaci gwamnatin jihar Taraba da ta gudanar da gagarumin bincike kan abun da ya bayyana a matsayin “Hare-haren wuce gona da iri da kisan gillar da aka yi wa al’ummar Hausawa."

Ya zama dole gwamnati ta hukunta masu laifi, Tullu

Ya kuma bukaci gwamnatin da ta tabbatar da ganin cewa an hukunta duk wadanda aka kama da hannu a lamarin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ci gaba da cewa:

"Al'ummar Hausawa sun dade suna zaman lafiya da makwabtansu yan Jukun, Chamba, Ichen, Kuteb da Tiv a Takum tsawon sama da shekaru 200.
"Sai dai kuma a baya-bayan nan mayakan Kuteb na yawan kaiwa al'ummar Hausawa hare-hare ba tare da wasu dalilai ba."

Ya ce kisan al'ummar Hausawa da mayakan Kuteb suka yi na huce takaici ne domin Hausawa a Takum ba su da alaka ko shiga rikicin da ke tsakanin Kuteb da Fulani makiyaya.

Kara karanta wannan

Rikicin Kabilanci: Hausawa Sun Nemi Abi Musu Kadu, Yayin da Wata Ƙabila Ta Kashe Musu Mutane 32

Tullu ya kuma yi zargin cewa daga ranar 11 ga watan Mayun 2022 har zuwa yau babu wani wata da zai shige ba tare da mayakan Kuteb sun farmaki Bahaushe ko kashe shi ba.

Al'ummar Hausawa na ba Fulani da suka addabi kabilar Kuteb mafaka - Kungiyar Kuteb ta yi martani

Rahoton ya kuma kawo cewa da yake martani, shugaban kungiyar Kuteb na kasa, Mista Emmanuel Ukwen, ya yi watsi da zargin kisan a matsayin mara tushe.

Ya kuma zargi Hausawa da ke Takum da ba Fulanin da suka addabi al’ummar Kuteb mafaka.

Ukwen ya ce ya gana da wakilan al’ummar Hausawa inda suka tattauna yadda za a samu zaman lafiya da fahimtar juna a tsakaninsu.

Yan Boko Haram Sun Yi Wa Mutane 15 Yankan Rago a Jihar Borno

A wani labari na daban, mayakan kungiyar ta'addanci na Boko Haram sun yi wa akalla mutane 15 yankan rago a wasu hare-hare da suka kai kan garuruwa biyu a karamar hukumar Jere ta jihar Borno.

Maharan sun farmaki kauyen Kofa da tsakar dare sannan suka fara harbi kan mai uwa da wahabi, wanda ya shafe kimanin awa daya zuwa safiyar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng