Sifetan Yan Sanda Ya Sa Labule da Kwamandojin Rundunar Yan Sanda a Abuja

Sifetan Yan Sanda Ya Sa Labule da Kwamandojin Rundunar Yan Sanda a Abuja

  • Sabon shugaban hukumar 'yan sanda ta ƙasa (IGP), Egbetokun, ya sa labule da kwamandojin runduna sama da 70 a hedkwatar da ke Abuja
  • Manyan jiga-jigan 'yan sanda irinsu mataimakan sifetan yan sanda ƙasa daga shiyyoyi 6 sun halarci taron ranar Litinin, 26 ga watan Yuni
  • Duk da babu wani bayani kan dalilin kiran wannan taro ana ganu ba zai alaƙa da yunkurin aabon IGP na kawo sauyi a lamarin taaron ƙasar nan

FCT Abuja - Mukaddashin sifetan 'yan sandan Najeriya, IGP Olukayode Egbetokun, na ganawa yanzu haka da kwamandojin rundunar 'Police Mobile Force' 79 a hedkwatar Abuja.

Jaridar Punch ta kawo rahoton cewa dukkan mataimakan sifetan 'yan sanda na ƙasa daga shiyyoyi Shida da ake da su a Najeriya (DIG) sun halarci taron na yau Litinin, 26 ga watan Yuni, 2023.

Kara karanta wannan

Karya Ta Kare: Hukumar EFFC Ta Cafke Sanata Kan Badakalar €5.7m

Mukaddashin sifetan yan sanda na ƙasa, IGP Olukayode Egbetokun.
Sifetan Yan Sanda Ya Sa Labule da Kwamandojin Rundunar Yan Sanda a Abuja Hoto: Policeng
Asali: Twitter

Haka nan kuma wasu daga cikin ƙananan mataimakan sifetan 'yan sanda na ƙaaa (AIG) sun samu halartar taron wanda ke gudana yanzu haka a birnin Abuja.

Rahoto ya nuna cewa IGP ya isa wurin taron da misalin ƙarfe 3:10 na rana, awanni biyu bayan asalin lokacin da aka tsara gudanar da taron watau ƙarfe 1:00 na tsakar rana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Menene maƙasudin wannan taro?

Har kawo yanzun babu wani cikakken bayani kan maƙasudin wannan zama ko muhimman batutun da taron zai maida hankali a kai.

Sai dai a wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sanda ya fitar ranar Lahadi, zaman na da alaƙa da kokarin tabbatar da tsaro a sassan Najeriya.

Sanarwan ta ce IGP Egbetokun ya bayyana cewa taron wani ɓangare ne na ɗamarar da ya ɗaura da nufin cimma kudirin dawo da tabbataccen zaman lafiya a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Rai Bakon Duniya: An Yi Babban Rashi Yayin Da Tsohon Kakakin Rundunar 'Yan Sandan Najeriya Ya Kwanta Dama

Ya kuma ƙara bai wa 'yan Najeriya tabbacin cewa rundunar 'yan sanda zata yi duk mai yuwuwa wajen tsare rayuka da dukiyoyinsu, kamar yadda Independent ta tattaro.

Malam Nuhu Ribaɗu Ya Fara Aiki a Matsayin Mai Bada Shawara Kan Tsaro

A wani rahoton na daban kun ji cewa Sabon mai bada shawara kan tsaron ƙasa da shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa ya kama aiki ranar Litinin.

Nuhu Ribaɗu ya karbi ragamar ofishin NSA daga hannun Manjo Janar Babagana Munguno mai ritaya a birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262