Shugaba Tinubu Zai Iso Najeriya Ranar Talata Domin Shagalin Sallah
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai dawo Najeriya ranar Talata domin gudanar da shagalin bikin babbar Sallah
- Shugaba Tinubu zai gudanar da shagalin bikin babbar Sallah a birnin Legas bayan ya dawo ana gobe Sallah wacce za a yi a ranar Laraba
- Shugaban ƙasar wanda da zai dawo Najeriya a ranar Asabar ya ɗage dawowarsa bayan ya shilla zuwa birnin Landan kai wata gajeruwar ziyara
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai dawo ƙasar nan daga tafiyar da ya yi zuwa ƙasar a ranar Talata, 27 ga watan Yunin 2023, idan har ba wani sabon sauyi aka samu ba.
Shugaban ƙasar zai shigo Najeriya ne ranar Talata ana gobe bikin shagalin babbar Sallah.
Wani majiya a kusa da fadar shugaban ƙasa ya tabbatarwa da Channels tv a ranar Lahadi cewa, shugaban ƙasar a birnin Legas zai yi hutun Sallah.
Kotun Zaben Shugaban Kasa: Jerin Manyan Kwararan Shaidun Da Atiku Ya Gabatar Kan Tinubu a Gaban Kotu Sun Bayyana
A cewar majiyar, tuni har an tura da tawaga zuwa birnin na Legas domin tarbar shugaban ƙasar idan ya duro Najeriya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Shugaba Tinubu ya shilla birnin Landan daga ƙasar Faransa
A ranar Juma'a, 24 ga watan Yuni Shugaba Tinubu ya kammala ziyarar da ta kai shi birnin Faris na ƙasar Faransa, inda ya halarci taron ƙoli na kuɗi na duniya da aka gudanar a ƙarƙashin jagorancin Emmanuel Macron, shugaban ƙasar Najeriya.
Tun da farko, an shirya cewa shugaban ƙasar zai dawo gida Najeriya ne a ranar Asabar, amma sai jirginsa ya shilla zuwa birrnin Landan na ƙasar Ingila domin wata ƴar gajeruwar ziyara ta ƙashin kansa.
Hadimin shugaban ƙasa, Dele Alake, ya bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Asabar cewa Shugaba Tinubu zai dawo Najeriya ne akan lokaci domin gudanar da shagulgulan bikin babbar Sallah da za a gudanar ranar Laraba.
Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Fasa Dawowa Gida Najeriya Daga Faransa, An Bayyana Inda Jirginsa Zai Shilla
Adesina Ya Yaba Da Kokarin Shugaba Tinubu
A wani labarin na daban kuma, shugaban bankin raya ƙasashen nahiyar Afirika, Akinwunmi Adesina, ya yaba da tsare-tsaren da Shugaba Tinubu yake yi akan tattalin arziƙin Najeriya.
Adesina ya bayyana hakan ne bayan ya gudanar da taro da Shugaba Tinubu a birnin Faris na ƙasar Faransa bayan kammala taron ƙoli na kuɗi na duniya da aka gudanar a ƙasar ta Faransa.
Asali: Legit.ng