Babban Jigon Jam'iyyar APC Ya Rasu Kasa Da Wata Daya Da Barin Mulki
- Jigo a jam'iyyar APC kuma tsohon sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Farfesa Abdullahi Shinkafi ya riga mu gidan gaskiya
- Ahmed Shinkafi shi ne ya sanar da rasuwar babban jigon na jam'iyyar APC a ranar Lahadi duk da bai bayyana abinda ya haddasa rasuwarsa ba
- Sai dai, Shinkafi ya bayyana cewa za a gudanar da Sallar Jana'izar mamacin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada da misalin ƙarfe 4:00 na ranar Lahadi
FCT, Abuja - Babban jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) kuma tsohon sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Farfesa Abdullahi Shinkafi, ya riga mu gidan gaskiya.
A cewar rahoron AIT, Ahmed Shinkafi shi ne ya sanar da labarin rasuwar mamacin a madadin iyalan jigon na jam'iyyar APC.
A kalamansa:
"Lallai ne, mu daga Allah muke kuma lallai ne mu zuwa gare shi muke komawa. Ina sanar da rasuwar Farfesa Abdullahi Muhammad Shinkafi a birnin tarayya Abuja."
'Yan Maza Sun Kwanta: Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Babban Farfesa a Najeriya Ya Koma Ga Mahaliccinsa
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An bayyana lokacin da za a yi masa Sallar Jana'iza
Ahmed Shinkafi ya kuma ƙara bayyana cewa za a yi Sallar Jana'izar marigayin a babban masallacin birnin tarayya Abuja da misalin ƙarfe 4:00 na yammacin ranar Lahadi, 25 ga watan Yunin 2023.
Shinkafi babban ƙusa ne a jam'iyyar APC ta jihar Zamfara wanda ya yi aiki a ƙarƙashin gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle.
Rasuwar Shinkafi na zuwa ne a daidai lokacin ake binciken gwamnatin da ya yi aiki a ƙarƙashinta kafin a hana gwamnatin ta su komawa kan madafun ikon mulkin jihar a zaɓen ranar 18 ga watan Maris na 2023.
Gwamnan jihar na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Dauda Lawal, wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar, yana takun saƙa da tsohon gwamna Matawalle.
Babban Farfesa a Jami'ar Jihar Legas, Lai Oso Ya Kwanta Dama
A wani labarin na daban kuma, an yi shiga jimami a jami'ar jihar Legas (LASU) bayan wani babban Farfesa a fannin koyar da ilmin aikin jarida ya kwanta dama.
Farfesa Lai Oso ya koma ga mahaliccinsa ne a wani mummunan hatsarin mota da ya auku da shi lokacin da yake dawowa daga wata tafiya da ya yi.
Asali: Legit.ng