Babban Farfesa a Jami'ar Jihar Legas, Lai Oso Ya Kwanta Dama

Babban Farfesa a Jami'ar Jihar Legas, Lai Oso Ya Kwanta Dama

  • An yi babban rashi na babban Farfesa a fannin koyar da ilmin aikin jarida a jami'ar jihar Legas (LASU)
  • Farfesa Lai Oso ya kwanta dama ne bayan ya gamu da mummunan hatsarin mota yayin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga wani taro
  • Farfesan yana ɗaya cikin manyan Farfesoshin da ake ji da su a fannin koyar da ilmin aikin jarida a Najeriya

Jihar Legas - Wani babban farfesa a fannin koyar da aikin jarida a jami'ar jihar Legas (LASU), Lai Oso, ya kwanta dama.

Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa, Farfesa Oso, mai shekara 67 a duniya, ya koma ga mahaliccinsa ne bayan wani mummunan hatsarin mota ya ritsa da shi a ranar Asabar.

Farfesa Lai Oso ya kwanta dama
Farfesa Lai Oso ya koma ga mahaliccinsa Hoto: Dailytrust.com
Asali: UGC

Farfesan ya gamu da hatsarin ne lokacin da yake dawowa daga jami'ar jihar Delta (DELSU) da ke a Abraka, bayan ya halarci wani taro, rahoton The Punch ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi Mai: Kungiyar Masu 'POS' Sun Sanar Da Sabon Farashin Cire Kudi, Suna Fatan Yan Najeriya Za Su Rungumi Canjin

Waye marigayi Farfesa Lai Oso?

Lai Oso farfesa ne a makarantar koyon aikin jarida ta jami'ar jihar Legas (LASU).

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kasance shugaban tsangayar makarantar koyon aikin jarida ta jami'ar LASU daga shekarar 2011 zuwa 2015. Shi ne shugaban ƙungiyar Association of Communication Scholars and Professionals of Nigeria (ACSPN).

Ya yi karatun digirinsa na farko a jami'ar jihar Legas inda ya karanci (B.Sc. Mass Communication), ya yi digirin digir a jami'ar Obafemi Awolowo, Ile-Ife (M.Sc International Relations) sannan ya yi digirin digirgir (Ph.D Mass Communication) a jami'ar Leicester a Ingila a shekarar 1977.

Marigayin ya yi aiki a matsayin mai kawo rahoto a Rediyo da kamfanin dillancin labarai na Najeriya sannan ya koyar da kwasakwasai da dama kan aikin jarida.

Tsohon Kakakin Rundunar 'Yan Sanda Ya Kwanta Dama

A wani labarin na daban kuma, tsohon kakakin rundunar ƴan sandan Najeriya, Frnk Odita, ya riga mu gidan gaskiya bayan ya koma ga mahaliccinsa.

Kara karanta wannan

Badakalar Takardar Makarantar Tinubu: Omokri Ya Bayyana Abun da Ya Bankado a Jami’ar Chicago, Ya Wallafa Wasika

Frank Odita ya yi bankwana da duniya ne yana da shekara 84 bayan ya yi fama da ƴar gajeruwar rashin lafiya. Tsohon kakakin ya mutu ne a asbitin koyarwa na jami'ar jihar Legas (LASUTH) inda ya yi jinya.

Frank kafin ritayarsa daga aiki ya kuma taɓa riƙe muƙamin kwamishinan ƴan sanda a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng