Adesina Ya Yi Alkawarin Marawa Tinubu Baya a Kokarinsa Na Karfafa Tattalin Arzikin Najeriya
- Akinwumi Adesina, shugaban bankin raya kasashen Afrika, ya gana da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a taron koli na kudi na duniya da aka yi a birnin Paris
- Adesina ya ce shugaban kasa Tinubu ya burge shi da kyawawan manufofinsa kan tattalin arzikin Najeriya
- Ya yi alkawarin marawa manufofin shugaban kasa Tinubu kan bunkasa da ci gaban tattalin arzikin Najeriya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Paris, Faransa - Shugaban bankin raya kasashen Afrika, Akinwumi Adesina, ya yaba ma jajircewar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wajen gina tattalin arziki mai karfi a kasar.
Adesina, wanda ya gana da shugaban kasa Tinubu yayin taron koli na kudi na duniya a birnin Paris, kasar Faransa, ya ce bankin ci gaban Afrika zai tallafawa hangen Tinubu kan tattalin arzikin Najeriya.
Ya bayyana hakan a cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter @akin_adesina a ranar Juma'a, 23 ga watan Yuni.
“Najeriya Na Gab Da Ganin Karshen Rashin Tsaro”, Buni Ya Magantu Kan Nadin Shugabannin Tsaro, Ribadu Da Tinubu Ya Yi
Ya rubuta:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Na yi wata babbar ganawa da Shugaba Tinubu a yayin taron koli na kudi na duniya a birnin Paris. Na gamsu da jajircewa da manufofinsa masu kyau kan tattalin arzikin Najeriya. Bankin raya kasashen Afirka zai bayar da gagarumin goyon baya ga manufofinsa kan tattalin arzikin Najeriya. @officialABAT."
Tinubu ya gana da yan Najeriya mazauna waje a kasar Faransa, hotuna da bidiyoyi sun bayyana
A baya mun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na cikin ganawa da yan Najeriya mazauna kasar waje a ranar Juma'a, 23 ga watan Yuni.
Wannan shine karo na farko da shugaban kasar ke ganawa da yan Najeriya mazauna waje a Faransa, a gefen taron duniya da ke gudana a birnin Paris, NTA News ta tabbatar.
An shawarci Tinubu kan wanda zai nada a matsayin sabon gwamnan CBN bayan dakatar da Emefiele
A wani labari na daban, mun ji cewa an shawarci shugaban kasa Bola Tinubu da ya dakatar da al'adar nan na nada ma'aikatan banki a matsayin gwamnonin babban bankin Najeriya (CBN), dadaddiyar al'adar babban bankin kasar.
Deji Adeyanju, wanda ya kasance dan fafutuka na Najeriya shine ya bayar da shawarar a wata wallafa da ya yi a Twitter a ranar Juma'a, 23 ga watan Yuni.
Asali: Legit.ng