Binciken Kwakwaf: Tsohon Ministan Tsaro, Janar Bashir Magashi Bai Mutu Ba
- Wani sakon WhatsApp da ya yadu ya yi ikirarin cewa Bashir Magashi, tsohon ministan tsaro ya mutu
- Sai dai kuma, kakakin tsohon ministan, Mallam Abdulkadir Muhammad, ya yi watsi da rahotannin
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya nada Magashi mai shekaru 73 a matsayin minista a ranar 21 ga watan 2019 kuma shi ne a kan kujerar har zuwa ranar 29 ga watan Mayu
Abuja - A kwanan nan ne ake ta rade-radin cewa tsohon ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi mai ritaya, ya rasu.
A cewar PR Nigeria, wani wallafa da aka yada a dandalin WhatsApp ya yi ikirarin cewa tsohon ministan tsaron, Manjo Janar Magashi ya mutu a ranar Juma'a, 23 ga watan Yuni.
Sanarwar ta ce:
"Mun samu labarin mutuwar mai girma Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, tsohon ministan tsaro. Ya kasance daya daga cikin masu kishin samun Najeriya sabuwa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Ya dace mu a matsayinmu na ’yan Adam mu nuna kauna da mutuntawarmu ga rayuwarsa, muna masu bakin ciki da mutuwarsa.
"Allah ya ji kansa da rahama, in shaaa Allah. Nagode."
Babu wani dalili da aka bayar da mutuwarsa.
Tsohon ministan tsaro, Janar Magashi bai mutu ba
Domin tabbatar da sahihanci ikirarin, PRNigeria ta tuntubi kakakin tsohon ministan, Mallam Abdulkadir Muhammad. Muhammad ya ce rahoton karya ne.
Jaridar ta nakalto Abdulkadir na cewa:
"Tsohon ministan tsaron, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi na nan da ransa kuma cikin koshin lafiya. Na yi magana da shi da iyalinsa ba da jimawa ba."
Labarin mutuwar Magashi kanzon kurege
Bisa ga amsar kakakin tsohon ministan tsaron, PRNigeria, ta yanke shawarar cewa labarin cewa Janar Magashi ya mutu kanzon kurege ne.
Jerin sunayen hafsoshin tsaro, IGP, da sauran nade-naden da Tinubu ya yi a hukumar tsaro
A baya mun ji cewa makonni uku da kama aikin shugabancin kasa, shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da yi wa shugabannin tsaro ritaya nan take a ranar Litinin, 19 ga watan Yuni.
Sauye-sauyen ya kuma shafi Sufeto Janar na yan sanda, manyan masu ba da shawara kan tsaro da kuma kwanturola janar na Kwastam yayin da aka sanar da madadinsu wadanda aka umurta da kama aiki a nan take.
Asali: Legit.ng