Sabon IGP Olukayode Egbetokun Ya Shiga Ganawa da Manyan Jami'ai a Abuja

Sabon IGP Olukayode Egbetokun Ya Shiga Ganawa da Manyan Jami'ai a Abuja

  • Muƙaddashin sifeta janar da 'yan sandan kasar nan, IGP Egbetokun ya shiga gana wa yanzu haka da manyan jami'an 'yan sanda a Abuja
  • Da yake jawabin buɗe taro, IGP ya jaddada kudirinsa na ƙara dankon alaka tsakanin 'yan sanda da sauran hukumonin tsaron Najeriya
  • Mahalarta taron sun haɗa da manyan mataimakan IG, kananan mataimakan sufeta janar, kwamishinonin 'yan sanda da sauran manyan jami'ai

FCT Abuja - Sabon mukaddashin shugaban hukumar 'yan sandan Najeriya, IGP Olukayode Egbetokun, na ganawa yanzu haka da mambobin kwamitin gudanarwa.

Jaridar Punch ta tattaro cewa taron wanda ya ƙunshi manya-manyan jami'an yan sanda daga faɗin ƙasar nan yana gudana ne a ɗakin taro da ke hedkwatar 'yan sanda, Abuja.

Mukaddashin shugaban rundunar 'yan sanda, Olukayode Egbetokun.
Sabon IGP Olukayode Egbetokun Ya Shiga Ganawa da Manyan Jami'ai a Abuja Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Da yake jawabi a wurin taron, IGP Egbetokun ya tuna wa yan sandan cewa kamata ya yi su hana faruwar aikata muggan laifuka maimakon kai ɗauki bayan abun ya faru.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Kashe Manoma, Sun Tafka Mummunar Ta'asa a Jihar Kaduna

IGP ya kuma ɗauki alkawarin cewa a zamanin mulkinsa, zai ƙara inganta walwala da jin daɗin jami'an 'yan sanda domin ƙara musu kwarin guiwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka nan ya ƙara jaddada shirinsa na yauƙaka dangantakar rundunar 'yan sandan Najeriya da sauran hukumomin tsaron ƙasar nan.

Manyan jami'an hukumar 'yan sanda da suka halarci taron a Abuja

Waɗanda aka hanga sun halarci ɗakin taron IG a hedkwatar sun ƙunshi manyan jami'an hukumar 'yan sanda tun daga mataimakan sifetan yan sanda (DIG) da kananan mataimakan sifeta na kasa (AIG).

Sauran sun kunshi kwamishinonin 'yan sanda (CP) daga dukkan jihohin Najeriya da sauran manyan jami'ai masu muƙami, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Wannan taro na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan sabon mukaddashin IGP ya karɓi ragamar hukumar 'yan sanda daga hannun tsohon IG, Usman Alkali Baba.

Kara karanta wannan

Matsalar Tsaro Ta Zo Karshe, Sabon Shugaban Rundunar Sojin Saman Najeriya Ya Kama Aiki Gadan-Gadan

A farkon makon nan, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa baki ɗaya hafsoshin tsaro ritaya kana ya sanar da sabbin waɗanda zasu maye gurbinsu.

Hukumar DSS Ta Tona Shirin ‘Yan Ta’adda a Lokacin Bukukuwan Sallah a Najeriya

A wani labarin kuma kun ji cewa Hukumar DSS ta ankarar da al’umma cewa akwai shirye-shirye da wasu miyagu su ke yi na kai wa wuraren bauta da filayen wasanni hari.

Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar yan sandan farin kaya, DSS, ya fitar da sanarwa cewa akwai yiwuwar ‘yan ta’adda su kai hare-hare kwanan nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262