Majalisar Dokokin Jihar Filato Ta Amince Wa Gwamna Muftwang Ya Karbo Bashin N15bn
- Majalisar dokokin jihar Filato ta amince da buƙatar gwamna Caleb Mutfwang ta karɓo bashin naira biliyan N15bn daga banki
- Kakakin majalisar, Honorabul Matthew Sule ne ya karanta takardar gwamnan a zaman yan majalisu ranar Alhamis, 22 ga watan Mayu
- A cikin takaradar, gwamnan ya yi bayanin cewa zai yi amfani da kuɗin wajen biyan ma'aikata albashi na kusan biliyan N11bn
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Plateau - A zaman jiya Alhamis, 22 ga watan Yuni, 2023, majalisar dokokin jihar Filato da ke Arewa ta tsakiya a Najeriya ta sahalewa mai girma gwamna ya karɓo bashin kuɗi daga banki.
Rahoton jaridar Daily Trust ya tattaro cewa majalisa ta amince da buƙatar gwamna Caleb Mutfwang ta ciyo wa jihar bashin kuɗi kimanin naira biliyan N15bn.
Gwamnan ya aike da takardar bukatar neman karɓo wannan bashin ga majalisar dokokin jihar ne da nufin amfani da kuɗin wajen biyan albashin ma'aikata da kuma siyo kayan noma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin majalisar dokokin, Honorabul Matthew Sule ne ya karanta takardar da gwamnan ya aiko ga sauran mambobin majalisar, inda ya nemi sahalewarsu domin karɓo bashin.
A cikin takardar da gwamna Mutfwang ya tura wa majalisar kuma kakaki ya karanta, ya yi bayanin cewa ma'aikata na bin gwamnati bashin albashi da suka kai biliyan N11bn.
Yadda gwamnan ya ɗauki matakai tun da ya karɓi mulki
Gwamna Muftwang na ɗaya daga cikin gwamnonin jam'iyyar PDP da suka samu nasarar kwace mulki daga hannu jam'iyyar APC a zaɓen ranar 18 ga watan Maris, 2023.
Tun bayan hawansa mulki ranar 29 ga watan Mayu, gwamnan ya ɗauki matakai daban-daban a gwamnati kama daga korarar hadiman da ya taras da sauransu.
Daga daga cikin manyan matakan da ya ɗauka bayan karɓan mulki daga Simon Lalong, shi ne dakatar da baki ɗaya shugabannin kananan hukumomin jihar Filato.
A cewarsa, ya ɗauki wannan matakin ne domin bada damar gudanar da bincike kan tuhumar da ake wa Ciyamomin, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Gwamna Aliyu Ya Kori Sakatarorin Ilimi Na Kananan Hukumomi 23 a Sakkwato
A wani rahoton na daban kuma Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu, ya kori Sakatarorin ilimi na kananan hukumomi 23 da ke faɗin jihar.
Wannan na zuwa ne yayin da shugaban makarantar Firamaren Sabon Birni ya bayar da shaida a gaban Kotun ƙarar zaben gwamna.
Asali: Legit.ng