Bikin Babban Sallah: Sanata Yari Ya Gwangwaje Makwabtansa Da Raguna 500
- Sanata Abdul’aziz Yari ya rabawa makwabtansa, marasa gata, da yan gudun hijira raguna 500 domin su yi bikin babban sallah a karamar hukumar Talata-Mafara
- Wannan kari ne a kan raguna 1,000 da shanaye 400 da tsohon gwamnan na zamfara ya rabawa jiga-jigan APC a jihar
- Nan da yan kwanaki daukaci al'ummar Musulmi za su yi bikin babban sallah inda ake yanka raguna da sauransu domin layya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Zamfara - Sanata Abdul’aziz Yari, mai wakiltan Zamfara ta yamma, ya rabawa makwabtansa da marasa karfi a garin Talata-Mafara da ke karamar hukumar Talata-Mafara ta jihar raguna 500 domin su yi bikin babban sallah.
Shugaban kwamitin rabon, Alhaji Sha’aya Sarkin-Fawa ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da ragunan ga wadanda suka ci moriyar shirin a ranar Alhamis, 22 ga watan Yuni, jaridar Daily Nigerian ta rahoto.
Da farko ya rabawa jiga-jigan APC a Zamfara raguna 1,000 da shanaye 400
Sarkin-Fawa ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Kun sani, wannan karamci ne da shugabanmu, Sanata Yari ya saba yi duk shekara domin taimakawa marasa karfi don su samu damar yin bikin babban sallah cikin sauki.
“Wannan na makwabtansa, marasa karfi, yan gudun hijira da marayu a garin Talata-Mafara ne kawai.
“Wannan kari ne a kan raguna 1,000 da shanaye 400 da ya raba da farko ga jagororin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matakan jihar, karamar hukuma da gudunmomi ta kungiyar siyasarsa."
Sarkin-Fawa, wanda ya kasance jigon jam’iyyar APC a jihar ya yaba ma tsohon gwamnan na Zamfara kan shirye-shiryensa daban-daban na tallafawa mutane a matakin farko.
Yay i kira ga Musulmai da su yi amfani da bikin babban sallah domin yi wa jihar da Najeriya addu’an samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Gwamnatin Kano ta ba dalibai mako guda a matsayin hutun babban sallah
A wani labarin, mun ji cewa ga'aikatar ilimi na jihar Kano ta amince da Juna'a, 23 ga watan Yuni, a matsayin ranar fara hutun bikin babban sallah ga dukkanin makarantun jeka ka dawo da na kwana a jihar.
Bikin babban sallan wanda zai shafe tsawon mako guda zai kare a ranar Asabar, 1 ga watan Yuni.
Saboda haka, ana sa ran daukacin daliban makarantun za su dawo makaranta a ranar Lahadi, 2 ga watan Yuni yayin da masu jeka ka dawo za su koma a ranar Litinin, 3 ga watan Yuni.
Asali: Legit.ng