Cire Tallafin Mai: 'Yan Kasuwa Sun Bayyana Kasashen Afirika Da Suka Fi Najeriya Tsadar Man Fetur

Cire Tallafin Mai: 'Yan Kasuwa Sun Bayyana Kasashen Afirika Da Suka Fi Najeriya Tsadar Man Fetur

  • A cewar ƙungiyar manyan dillalan man fetur ta Major Oil Marketers Association of Nigeria (MOMAN), farashin man fetur a Najeriya ya fi na ko ina arha a Afirika
  • MOMAN ta bayyana sauran ƙasashen Afirika suna siyar da man fetur fiye da farashin da ake siyar da shi a Najeriya
  • Masu sharhi sun bayyana cewa duk da hakan akwai damar yin fasa ƙwaurin man fetur ɗin zuwa wasu ƙasashen Afirika

A cewar wasu bayanai daga ƙungiyar manyan dillalan man fetur ta Major Oil Marketers Association of Nigeria (MOMAN), farashin man fetur ya fi arha a Najeriya idan aka kwatanta da wasu ƙasashen musamman na Yammacin Afirika.

Bayanan na zuwa ne duk da tumɓuke tallafin man fetur da gwamnatin Bola Tinubu ta yi a Najeriya.

Kasashen da man fetur yake da tsada fiye da Najeriya
Man fetur na da arha sosai a Najeriya Hoto: MOMAN
Source: Facebook

Har yanzu Najeriya ce ke siyar da man fetur a farashi mafi arha a nahiyar Afirika

Kara karanta wannan

Jihar Imo Da Sauran Jerin Jihohin Da Aka Fi Siyan Man Fetur Da Dankaran Tsada a Najeriya

Bayan cire tallafin man fetur, kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) ya mayar da farashin litar mai zuwa N488 kan kowacce lita inda sauran masu siyar da man fetur ɗin suka kwaikwayi matakin na kamfanin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nairametrics ta rahoto cewa sauran ƴan kasuwar na siyar da man fetur ɗin akan farashin N500 zuwa N510 kan kowace lita, wanda hakan ya nuna har yanzu farashin yana da arha idan aka kwatanta da sauran wasu ƙasashen nahiyar Afirika.

Bayanan da MOMAN ta fitar sun nuna yadda farashin man fetur yake a wasu ƙasashe 12 na nahiyar Afirika.

Ga jerinsu kamar haka:

  • Najeriya: N488 – N570 kowace lita a jihohin ƙasar
  • Cameroon: N906 duk lita ɗaya
  • Benin Republic: N807.85 duk lita ɗaya
  • Serra Leone: N822.95 duk lita ɗaya
  • Togo: N868.25 duk lita ɗaya
  • Burkina Faso: N1057 duk lita ɗaya
  • Ivory Coast: N1011.70 duk lita ɗaya
  • Ghana: N890.90 duk lita ɗaya
  • Guinea: N1049.45 duk lita ɗaya
  • Mali: N1079.65 duk lita ɗaya
  • Senegal: N1230.65 duk lita ɗaya
  • Liberia: N762.55 duk lita ɗaya

Kara karanta wannan

"Babu 'Yan Najeriya a Ciki, Attajiran Nahiyar Afirika 4 Suka Yi Alkawarin Sadaukar Da Kaso 50% Na Dukiyarsu

Jihohin Da Man Fetur Ya Fi Tsada a Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa a watan Mayun 2023 ƴan Najeriya sun siya man fetur da ɗan karan tsada bayan ya ƙaru kaso 37.57% daga kan N173.08 a watan Mayun 2022 zuwa N238.11 a watan Mayun 2023.

Jihar Imo ita ce akan gaba a cikin jerin jihohin da farashin na man fetur ya fi tsada a ƙasar nan a watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng