Magidanci Ya Maka Surikansa Kara Gaban Kotun Musulunci a Jihar Kano

Magidanci Ya Maka Surikansa Kara Gaban Kotun Musulunci a Jihar Kano

  • Wani magidanci ya fusata ya kai ƙarar iyayen matarsa ƙara a gaban kotun shari'ar musulunci da ke a jihar Kano
  • Magidancin yana ƙararsu ne bisa zargin sun ɗauke masa mata daga gidansa ba tare da izninsa ba zuwa wani waje
  • Sai dai, matar ta musanta hakan inda ta bayyana cewa da ƙashin kant ta sulale daga gidansa saboda rashin kulawar da yake bata

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Wani magidanci mai shekara 34 a duniya, Kabiru Muhammad, ya maka surikansa gaban kotun shari'ar musulunci mai zamanta a jihar Kano bisa zargin ɗauke masa mata daga gidansa.

Magidancin dai yana zargin surikan nasa da laifin tafiya masa da mata ba tare da izninsa ba, cewar rahoton Daily Trust.

Magidanci ya maka surikansa kotu
Magidancin yana zarginsu da dauke masa mata daga gida Hoto: Punch.com
Asali: UGC

Mai shigar da ƙarar ya maka mutum uku ne a gaban kotun waɗanda duk ƴan uwan matarsa ne. Kabiru yana ƙarar iyayen matar tasa, Ali Dan Abba da Hadiza Dan Abba da wani Haruna Bala Dangwauro, a gaban kotun mai zamanta a unguwar Hotoro Masallachi a cikin Kano Municipal.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida Ya Sake Bankado Wata Badakalar Ganduje, Ya Bayar Da Wani Muhimmin Umarni

A ƙashin kanta ta bar gidan mijin nata

Sai dai, a lokacin da ake sauraron ƙarar, matar ta gayawa kotun cewa babu wanda ƴa ɗauketa daga gidansa, kawai dai ta tafi gidan yayarta ne saboda mijinta ya kasa kulawa da ita.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Alƙalin kotun Mallam Nasir Muhammad Ahmad, ya bayar da umarnin akai matar zuwa asibiti domin duba lafiyarta kafin a ci gaba da sauraron ƙarar.

Bayan kammala zaman kotun, matar ta yi magana da manema labarai inda ta bayyana cewa da ƙashin kanta ta bar gidan mijin nata ba tilasta mata yin hakan akai ba.

Tace ta daɗe tana fama da matsanancin rashin lafiya amma mijin nata ya ƙi kai ta zuwa asibiti a duba lafiyarta.

A kalamanta:

"Ni ce na kai kaina gidan yayata. Babu wanda ya tilasta min na yi hakan. Na daɗe ina fama da rashin lafiya amma ya ƙi kai ni zuwa asibiti. Hakan ya sanya na tafi gidan yayata a ƙaramar hukumar Dambatta."

Kara karanta wannan

Wata Mata Ta Nemi Kotu Ta Gintse Aurenta Na Shekaru 14 Da Mijinta, Ta Bayar Da Dalili

Matar Aure Ta Nemi Kotu Ta Datse Igiyar Aurenta

A wani labarin na daban kuma, wata matar aure ta nemi kotu da ta raba aurenta da mijinta wanda suka kwashe shekara 14 suna tare.

Matar auren ta koka da cewa auren na su ya koma wanda babu so da ƙauna a ciki saboda haka ta ke son rabuwa da mijin nata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng