Majalisar Dokokin Jihar Benue Ta Dakatar Da Shugabannin Kananan Hukumomin Jihar

Majalisar Dokokin Jihar Benue Ta Dakatar Da Shugabannin Kananan Hukumomin Jihar

  • Majalisar dokokin jihar Benue ta dakatar da gaba ɗaya shugabannin ƙananan hukumomin jihar daga muƙamansu
  • Majalisar ta ɗauki wannan matakin biyo bayan zargin yin sama da faɗi da dukiyar al'umma da ake zargin shugabannin da shi
  • Majalisar za kuma ta binciki lokacin da shugabannin suka kwashe akan mulki domin duba kuɗaɗen da suka samu da yadda suka yi amfani da su

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Benue - Majalisar dokokin jihar Benue ta bayar da shawarar dakatar da shugabannin ƙananan hukumomi 23 na jihar bisa zargin almubazzanci da kuɗi, cewar rahoton Daily Trust.

Kakakin majalisar, Aondona Dajoh, ya sanar da dakatar da su a yayin zaman majalisar, bayan duba rahoton kwamitin wucin gadi da aka kafa domin bincikar kuɗin da suka samu da yadda suka kashe su wanda gwamnan jihar ya aike mata da shi.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta Dakatar Da Shugabannin Kananan Hukumomi 23 a Wata Jihar Arewa, Ta Fadi Dalili

Majalisar dokokin jihar Benue ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi
Ana zargin shugabannin da wawurar dukiya Hoto: Arisetv.com
Asali: UGC

Dajoh ya bayyana dakatarwar ta zama tilas domin bayar da dama majalisar ta gudanar da cikakken bincike kan kuɗaɗen shigan da suka samu da yadda suka yi amfani da su, cewar rahoton The Punch.

Ana zargin shugabannin da sama da faɗi da dukiyar al'umma

Ƴan majalisar sun kuma amince su faɗaɗa bincikensu zuwa gaba ɗaya lokacin da shugabannin ƙananan hukumomin suka yi akan mulki, bayan sun gano cewa a rahoton na wata uku da aka basu, akwai baɗakalar kuɗi sosai a ciki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tun da farko, shugaban kwamitin wucin gadin, Peter Ipusu, ya bayyana cewa kwamitinsa ya gano cewa shugabannin ƙananan hukumomin 23 sun tafka almundahanar kuɗi sosai.

Hakan a cewarsa ya sanya suka shawarci majalisar da ta amince da ƙudirin kira ga gwamnan jihar ya dakatar da su domin gudanar da bincike kan kuɗaɗen da suka shigo musu da yadda suka yi amfani da su.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida Ya Sake Bankado Wata Badakalar Ganduje, Ya Bayar Da Wani Muhimmin Umarni

Za a Binciki Tsohon Gwamnan Benue

A wani labarin na daban kuma, gwamnan jihar Benue, Rev Fr. Hyacinth Alia ya kafa wani babban kwamiti wanda zai ƙwato kadarorin jihar da gwamnatin Samuel Ortom ta yi awon gaɓa da su.

An ɗora wa kwamitin alhakin ƙwato duk wata kadara ta gwamnatin jihar wacce aka rabar da ita ba bisa ƙa'ida ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng