Yan Bindiga Sun Banka Wa Mutane 11 Wuta Har Suka Mutu a Jihar Filato

Yan Bindiga Sun Banka Wa Mutane 11 Wuta Har Suka Mutu a Jihar Filato

  • Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai farmaki mai muni, sun babbake mutane 11 a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato
  • Wani mazaunin ƙauyen Chisu, ya ce maharan sun kona gidaje, coci da kadraron mutane gabanin su yi gaba
  • Wata majiya daga hedkwatar 'yan sanda da ke Jos ta ce tuni hukumar ta tura ƙarin dakaru domin shawo kan lamarin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Plateau - Wasu 'yan ta'adda da suka kai farmaki kauyen Chisu da ke ƙaramar hukumar Mangu a jihar Filato ranar Talata da daddare, sun ƙona mutane 11 har lahira.

Rahoton Punch ya nuna cewa mutanen sun ruga zuwa cikin wani gida domin tseratar da rayuwarsu bayan sun ji karar harbe-harben 'yan ta'addan da misalin ƙarfe 11:00 na dare.

Harin yan bindiga a jihar Filato.
Yan Bindiga Sun Banka Wa Mutane 11 Wuta Har Suka Mutu a Jihar Filato Hoto: punchng
Asali: Facebook

Amma duk da haka maharan suka bi su har gidan da suka ɓuya, suka banka musu wuta, wanda hakan ya yi sanadin mutuwarsu.

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wata Mata Manajar Banki, Sun Dade Suna Yi Mata Gargadi

Wani mazaunin garin Chisu, wanda ya samu nasarar tsira daga harin ya tabbatar da kisan mutanen ga jaridar a Jos, babban birnin jihar Filato, ranar Laraba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar Mista Bulus, yan bindigan sun kuma kona wata Majami'a da ke kan titin Mangu-Bokkos da wasu kadarori kafin daga bisani su kama gabansu.

A ruwayar Daily Post, Bulus ya ce:

"Yan ta'adda sun kai farmaki ƙauyen Chisu da ke ƙaramar hukumar Mangu a daren jiya da misalin ƙarfe 11:00. Lokacin da suka shiga, sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi."
"Bisa haka mutane suka fara gudun neman tsira, wasu suka shiga gidan shugaban ƙauye, wanda bisa rashin sa'a maharan suka banka masa wuta kuma da safiyar nan aka ciro gawarwakin mutum 11 da suka ƙone."
"Yan ta'addan sun kuma ƙone cocin COCIN Regional da ke titin Mangu zuwa Bokkos tare da wasu gidaje, motoci da Keke Napep kafin daga bisani su yi gaba."

Kara karanta wannan

Da Dumi-ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Harbe Babban Ma'aikacin INEC Har Lahira, Sun Sace Matarsa

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan Filato, Alabo Alfred, bai ɗaga kiran waya da aka masa ba yayin da aka tuntuɓe shi kan sabon harin.

Amma wata majiya daga hedkwatar 'yan sanda da ke Jos ta ce tuni aka ƙara tura jami'an tsaro yankunan da lamarin ya faru bayan samun rahoto.

Yan Bindiga Sun Sheka Barzahu Yayin da Suka Kai Wa Jami'an Tsaro Hari

A wani labarin na daban kuma Wasu 'yan bindiga 15 sun kwashi kashinsu a hannun dakarun 'yan banga a yankin ƙaramar hukumar Ihiala ta jihar Anambra.

Kakakin hukumar yan sandan Anambra ya ce yayin musayar wuta 'yan banga suka halaka 'yan bindiga biyu kuma suka kwato makamai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262