Shugabannin Tsaro: “Girman Kan Tinubu Zai Jefa Shi a Matsala” – Charly Boy

Shugabannin Tsaro: “Girman Kan Tinubu Zai Jefa Shi a Matsala” – Charly Boy

  • Shararren mawakin Najeriya Charly Boy ya bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya sassauta a matakan da yake dauka
  • Yayin da yake caccakar yan Najeriya kan jinjinawa Tinubu da suke yi, Charly Boy ya bukaci shugaban kasar da ya yi taka-tsa-tsan a duk abubuwan da yake yi
  • Wasu jama'a na ta jinjinawa Tinubu kan sauye-sauten da yake yi a majalisarsa cikin makonni uku ce kacal, sai dai Charly Boy ya ce Tinubu ba zai iya kange Najeriya ydda ya yi wa Lagas ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Fitaccen mawakin Najeriya kuma jarumin fim Charles Oputa wanda aka fi sani da Charly Boy ya yi martani a kan tsige shugabannin tsaro da nada sabbi da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi.

A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter, Charly Boy ya nuna rashin jin dadinsa ga yan Najeriya da suke jinjinawa shugaban kasar kan yadda yake tafiyar da harkokin gwamnati a baya-bayan nan.

Kara karanta wannan

“Baba Tinubu Lokacinmu Ne Mu Zama Ministan FCT”: Yan Asalin Abuja Sun Koka

Charly Boy da Shugaban kasa Bola Tinubu
Shugabannin Tsaro: “Girman Kan Tinubu Zai Jefa Shi a Matsala” – Charly Boy Hoto: Charly Boy Area Fada 1 @AreaFada1, Facebook: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Girman kan Tinubu zai jefa shi a matsala - Charly Boy

A cewarsa, abun da shugaban kasar yake yi don kawai ya samu karbuwa ne a wajen yan Najeriya yayin da yake janye hankalinsu don ya cimma babban manufarsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Charly Boy ya rubuta

"Ni kadai ina ta yiwa wawayen da ke tafawa TINUBU dariya.
"Da yawanmu mun san cewa duk wadannan abubuwa da yake yi bige ne."

Zai iya kange Lagas amma ba Najeriya ba, Charly Boy

Da yake ci gaba da jawabi, mawakin ya bayyana yan Najeriya da ke jinjinawa Tinubu a matsayin "wawaye" yayin da ya bayyana cewa idan shugaban kasar bai yi hankali ba, zai shiga gagarumin matsala.

Mawakin ya kara da cewar:

"Amma girman kansa da yin duk yadda ya ga dama zai kai shi ga matsala.
"Yana iya kange Lagas amma ba Najeriya ba.

Kara karanta wannan

Muhammadu Sanusi II Ya Fayyace Dalilan Zuwa Aso Rock da Abin da Ya Fadawa Tinubu

"Duk wadannan yunkuri na damfara an yi su ne don ciye zukatan jama'a da samun karbuwa a wajen wawayen yan Najeriya da janye hankalinsu yayin da yake cimma babban kudirinsa."
"Kada ku ce AreaFada bai fada mana ba."

Jerin sunayen shugabannin tsaro, IGP da sauran nade-nade da Tinubu ya yi

A wani labarin, Legit.ng ta kawo a baya cewa makonni uku da kama aikin shugabancin kasa, shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da yi wa shugabannin tsaro ritaya nan take a ranar Litinin, 19 ga watan Yuni.

Sauye-sauyen ya kuma shafi Sufeto Janar na yan sanda, manyan masu ba da shawara kan tsaro da kuma kwanturola janar na Kwastam yayin da aka sanar da madadinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: