An Shiga Rudani, A Yayinda 'Yan Bindiga Suka Sace Basarake Da Mai Dakinsa A Kogi
- 'Yan bindiga sun yi garkuwa da Oba na Idofin, Shedrack Durojaiye Obibeni da matarsa a ƙaramar hukumar Yagba ta Gabas da ke jihar Kogi
- Lamarin ya faru ne a kan hanyar Makutu zuwa Idofin a jihar ta Kogi da misalin ƙarfe 5 na yammacin ranar Litinin
- Shugaban ƙaramar hukumar Yagba ta Gabas, Abdulrasak Asiru, ya bayyana lamarin a matsayin abin ban tsoro da takaici, inda ya bayyana aniyarsa ta ceto basaraken
Kogi - Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun ɗauke Oba na Idofin, Shedrack Durojaiye Obibeni, da mai ɗakinsa a karamar hukumar Yagba ta Gabas da ke jihar Kogi.
An yi garkuwa da mutanen ne a hanyar Makutu zuwa Idofin da ke jihar ta Kogi da misalin karfe 5 na yammacin ranar Litinin, kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya bayyana.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Mista Abdulrasak Asiru, shugaban ƙaramar hukumar Yagba ta Gabas, ya bayyana lamarin a matsayin abin ban tsoro da takaici.
Kusan shekara 2 kenan rabon yankin da masu garkuwa da mutane
The Punch ta ruwaito Asiru yana cewa, har yanzu yana cikin kaɗuwa kan lamarin da ya kai kusan shekaru biyu bai faru ba a yankin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A kalaman shugaban ƙaramar hukumar:
“A matsayina na shugaban ƙaramar hukumar da sauran al’ummar yankin Yagba ta Gabas, mun yi matukar kaɗuwa bisa sace mana Oba da matarsa da aka yi da yammacin yau.”
“Dalili kuwa shi ne mu a wannan karamar hukumar muna da ingantaccen shiri a ɓangaren tsaro, ta yadda muke sa ido gami da fatattakar duk wasu masu aikata miyagun laifuka.”
“Wannan lamarin ya kasance shiryayyen abu da masu garkuwa da mutane suka daɗe suna shiri akai, domin a bayanin da na samu, Oba da matarsa sun ɗan fita ne kawai domin ganin wani abu, amma a ƙasa da mintuna 10, har mummunan lamarin ya faru.”
"Muna zargin akwai wata ƙullalliya game da lamarin mai ban takaici, amma ba za mu zauna ba har sai mun kai ga miyagun domin ceto sarkin namu da matar tasa."
Mutane sun bazama neman basaraken a jeji
Shugaban karamar hukumar ya ce tuni suka aika da saƙo zuwa ga ɗaukacin sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma na yankin Okun, kan su sanya idanu gami da aiwatar da bincike domin ceto basaraken.
Asiru ya ƙara da cewa yanzu haka mafarautansu da 'yan banga sun bazama cikin jeji domin ceto mutanen da aka ɗauke, kamar yadda ya zo a rahoton The Cable.
Sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, SP Williams Ovye-Aya, ya ce har yanzu DPO na yankin da lamarin ya shafa bai yi masa bayani ba.
Dubun wasu ƙwararrun barayin awaki ta cika a Gombe
A wani labari da Legit.ng ta wallafa a baya, kun karanta cewa rundunar 'yan sandan jihar Gombe ta sanar da kama wasu matasa uku da suka ƙware wajen satar awakin jama'a.
Da Dumi-Dumi: Mummunan Hatsarin Mota Ya Ritsa Da Fasinjoji Da Dama a Wata Jiha, Rayuka Masu Yawa Sun Salwanta
Matasan kan yi amfani da babura masu ƙafa uku ne wajen gudanar da ayyukan sace-sacen da suka addabi cikin garin Gomben da su.
Asali: Legit.ng