Rusau Da Wasu Muhimman Matakai Da Gwamnoni Suka Dauka a Cikin Kwana 20 Da Hawa Mulki

Rusau Da Wasu Muhimman Matakai Da Gwamnoni Suka Dauka a Cikin Kwana 20 Da Hawa Mulki

  • Kwanaki 20 bayan hawa kan mulki, wasu gwamnonin jihohi sun ɗauki wasu muhimman matakai domin fara mulkinsu da su
  • Zaman gida na tilas da ake yi ranar Litinin a jihar Enugu, gwamnatin Peter Mbah ta kawar da shi da gaggawa
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf da takwaransa na jihar Niger, Mohammed Bago sun duƙufa rusau a jihohinsu ba kama hannun yaro

Abuja - Bayan ɗarewa kan mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023, wasu gwamnonin jihohi sun fara aiki gadan-gadan ba kama hannun yaro.

Kamar yadda rahoton The ICIR ya nuna, gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu, a cikin kwana 20 sun rushe naɗe-naɗen da gwamnonin da suka gabacesu suka yi.

Matakan da sabbin gwamnoni suka dauka bayan kwana 20 a ofis
Wasu daga cikin sabbin gwamnonin sun dauki muhimman matakai Hoto: Caleb Mutfwang/ Rev'd father hyacinth alia/Peter Mbah
Asali: Facebook

A jihar Cross River, gwamna Bassey Otu, ya bayar da umarnin a tantance ma'aikatan gwamnati da ke aiki a jihar.

Kara karanta wannan

Matsalar Tsaro: Gwamna Lawal Ya Fara Ɗaukar Matakan Kawo Karshen Yan Bindiga a Zamfara

Gwamnan jihar Enugu ya haramta zaman gida na ranar Litinin wanda ƙungiyar ƴan awaren Biafra (IPOB) ta tilasta a jihar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jihohin Niger da Kano ana ta Rusau

Rusau ba ƙaƙƙautawa shi ne abinda al'ummar jihohin Kano da Niger suka gani tun bayan rantsar da gwamna Abba Kabir Yusuf da gwamna Mohammed Umar Bago.

Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ya soke ƙwangilar aikin hanya da gwamnatin da ta gabace shi ta bayar.

Gwamna Francis Nwifuru, ya kafa tarihi a jihar Ebonyi bayan ya zaɓi mace ta farko, Grace Umezurike a matsayin sakatariyar gwamnatin jihar (SSG).

Gwamnan jihar Abia, Alex Otti ya sanya dokar ta ɓaci a fannin kula da shara na jihar da ke yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

A ƙoƙarin kare lafiya da dukiyar al'ummar jihar Kebbi, gwamna Nasir Idris Kauran Gwandu, ya biya dukkanin bashin kuɗaɗen alawus da jami'an tsaro ke bin jihar.

Kara karanta wannan

Gwamna Radɗa Ya Jagoranci Gwamnoni 6 Sun Gana da Tinubu Kan Muhimman Abu 2 da Suka Shafi 'Yan Arewa

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare, ya bayar da umarnin a binciki tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle.

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya soke filayen da aka bagar kafin ya zama gwamna.

Gwamnan jihar Taraba, Dr. Agbu Kefas, ya sanya dokar ta ɓaci a ɓangaren ilmi na jihar.

Ba wasu abubuwa bane sosai suka faru a jihohin Kaduna, Jigawa, Akwa Ibom da Delta ba.

Abba Gida-Gida Ya Yi Magana Kan Rusau Din Da Yake a Kano

A wani labarin gwamnan jihar Kano Abba Ƙabir Yusuf ya fusata kan yadda aka rabawa wasu ƴan tsiraru a jihar filayen makarantu.

Gwamnan ya bayyana cewa mai ɗakin tsohon gwamnan jihar ta mallaki filaye da yawa daga cikin waɗanda aka rabar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng