Babbar Sallah: Hutun Sallah Da Sauran Ranakun Hutu 4 Da 'Yan Najeriya Za Su Yi Zuwa Karshen Shekarar 2023
A yanzu haka dai Musulman Najeriya dama sauran 'yan Najeriya baki ɗaya, na dakon Gwamnatin Tarayya ta sanar da ranakun hutun da ta ware domin shagulgulan bikin Sallah mai zuwa.
Ranakun da gwamnatin za ta bayar na nufin ba za a gudanar da ayyuka a ma'aikatun gwamnati, makarantu, bankuna, kasuwanni da sauransu ba a cikinsu.
Ana sa ran za a gudanar da bikin babbar sallah a Najeriya a ranar Laraba 28 ga watan Yuni. Ranar Larabar da kuma Alhamis 29 ga watan Yuni, za su kasance ranaku biyu na hutun babbar sallar ta bana.
Ranakun hutun da za a yi a Najeriya zuwa ƙarshen shekarar 2023
Legit.ng ta tattaro muku sauran ranakun hutun da ‘yan Najeriya za su yi daga nan har zuwa ƙarshen shekarar 2023, ga ranakun kamar haka:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
1. Laraba, 28 ga watan Yuni – Ranar farko ta hutun babbar sallah.
2. Alhamis, 29 ga watan Yuni – Rana ta ta hutun babbar salla.
3. Laraba, 27 ga Satumba – Hutun bikin Maulidi.
4. Lahadi, 1 ga watan Oktoba – Ranar tunawa da samun ‘yancin kai, Litinin, 2 ga watan Oktoba – Ranar hutun ‘yancin kai (saboda ranar tunawa da ’yancin kai ta faɗo a ranar Lahadi).
5. Litinin, 25 ga watan Disamba - Ranar Kirisimeti.
6. Talata, 26 watan Disamba – Ranar Dambe ta duniya.
Yadda Gwamnatin Tarayyar Najeriya ke sanar da ranakun hutu ga 'yan ƙasa
Ma'aikatar harkokin cikin gida ce aka ɗorawa alhakin sanar da ranakun hutu ga 'yan Najeriya, in ji wani rahoto da BBC Pidgin ta wallafa.
Ma'aikatar na sanar da ranakun da Gwamnatin Tarayya ta ware a matsayin ranakun hutu ga 'yan ƙasar baki ɗaya.
Hakanan, duk wata ranar hutun da ta faɗo a cikin kwanakin ƙarshen mako, za a ayyana ranar mako ta gaba a matsayin ranar hutun.
Dalili kuwa shi ne domin a mayar da ranar hutun a cikin kwanakin aiki, saboda mutane sun riga da sun saba da hutawa a ranakun ƙarshen mako.
Sarkin Musulmi ya sanar da ranar Idin babbar sallah
A baya Legit.ng ta rahoto cewa mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ayyana ranar Laraba 28 ga watan Yuni a matsayin ranar Idin babbar sallah na shekarar 1444 AH/2023.
Sarkin Musulmi, wanda shine shugaban majalisar ƙoli ta addinin Musulunci ta Najeriya, ta hannun fadar sarkin da ke Sokoto, ya bayyana hakan a daren Lahadi, 18 ga watan Yuni, a wani sako da Legit.ng ta tsinkayo a shafin kwamitin ganin wata na Tuwita.
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin a matsayin ranar hutun dimokuraɗiyya
A kwanakin baya 'yan Najeriya sun mori ranar hutun dimokuraɗiyya da Gwamnatin Tarayya ta bayar a ranar Litinin, 12 ga watan Yunin shekarar 2023 da muke ciki.
Ana dai yin bikin ita wannan rana ta dimokuraɗiyya ne domin tunawa da irin gwagwarmayar da 'yan baya suka sha wajen ganin cewa dimokuraɗiyya ta kafu da ƙafafuwanta a Najeriya.
Asali: Legit.ng