Ku San Manya: Jerin Mataimakan Shugabannin Majalisar Dattawa 4 da Aka Yi a Najeriya

Ku San Manya: Jerin Mataimakan Shugabannin Majalisar Dattawa 4 da Aka Yi a Najeriya

FCT, Abuja - Kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa ita ce ta biyu mafi girma a majalisar dattawan Najeriya. 'Yan siyasa biyar ne suka rike wannan mukami tun bayan da kasar ta koma kan tafarkin dimokradiyya a 1999.

Legit.ng ta ruwaito cewa, mukamin babba ne a zauren majalisar dokokin kasar - wanda yake na biyu bayan na shugaban majalisar dattawa.

Mataimakan shugabannin majalisar Najeriya
Jerin wadanda suka taba rike mukamin mataimakin shugaban majalisar dattawa | Hoto: Atiku Abubakar, Ike Ekweremadu, Senator Ovie Omo-Agege, Senator Barau Jibrin
Asali: Facebook

Wanene mataimakin shugaban majalisar dattawa a Najeriya?

1. Barau Jibrin (Daga Arewa maso Yamma) - Yunin 2023 zuwa yau

Mataimakin shugaban majalisar dattawa na yanzu dai shi ne Barau Jibrin na jam’iyyar APC mai mulki, wanda ya kau kujerar bayan da akasarin ‘yan majalisar dattawa suka zabe shi kwanan nan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shi ne dan majalisa mai wakiltar mazabar Kano ta Arewa, yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Mambobin APC Sun Ɓarke da Zanga-Zangar Adawa da Sabon Kakakin Majalisa, Sun Faɗi Dalili

Mataimakin shugaban majalisar dattawa ne ke jagorantar majalisar dattawa a duk lokacin da babu shugaban majalisar.

Legit.ng ta tattaro jerin magabatan Sanata Barau:

2. Ovie Omo-Agege - Yunin 2019 zuwa Yunin 2023

Omo-Agege ya rike mukamin mataimakin shugaban majalisar dattawa daga shekarar 2019 zuwa 2023.

Ya kasance Sanata mai wakiltar Delta ta Tsakiya daga 2015 zuwa Yunin 2023. Shi dai asalin jihar Delta ne, yankin Kudu maso Kudu.

3. Ike Ekweremadu (Kudu maso Gabas) - Yunin 2015 zuwa Yuni 2019

Ekweremadu ya fito ne daga jihar Enugu kuma yayi aiki a majalisar dattawa, inda ya wakilci Enugu ta Yamma daga ranar 3 ga watan Yunin 2003 zuwa ranar 5 ga Mayun, 2023.

Dan jam’iyyar PDP ne, kuma ya kasance mataimakin shugaban majalisar dattawa na majalisar dattawa uku a jere (ta 6, 7 da 8).

A halin yanzu, yana kurkuku a Burtaniya (UK).

4. Ekweremadu (Kudu maso Gabas) - Yunin 2011 zuwa Yunin 2015

Kara karanta wannan

Cikakken Jerin Sunayen Shugabannin Majalisun Tarayya Na 10, Muƙamai, Da Jihohin Da Suka Fito

Ekweremadu shi ne mataimakin shugaban majalisar dattawa na majalisa ta 7.

5. Ekweremadu (Kudu maso Gabas) - Yunin 2007 zuwa Yunin 2011

Dan majalisar mai sarautar Dike Eji Eje Mba 1 na Oduma ya rike mukamin mataimakin shugaban majalisar dattawa a majalisar ta 6.

6. Ibrahim Mantu (Arewa ta Tsakiya) - Yunin 2003 zuwa Yunin 2007

Marigayi Mantu ya rike mukamin mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya tsakanin 2003 zuwa 2007.

An haifi Mantu a kauyen Chanso da ke gundumar Gindiri a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato a Arewa ta Tsakiyar Najeriya.

7. Ibrahim Mantu (Arewa ta Tsakiya) - Agustan 2000 zuwa Yunin 2003

Mantu ya kuma sake rike wannan babban mukami tsakanin shekarar 2003 zuwa 2007, a zamanin mulkin PDP.

8. Haruna Abubakar (Arewa-tsakiyar) - Yuni zuwa Agustan 2000

An zabi marigayi Abubakar zuwa majalisar dattawa don wakiltar mazabar Nasarawa ta Kudu a jihar Nasarawa a farkon jamhuriya ta hudu, inda ya tsaya takara a jam’iyyar PDP. Ya fara aiki a ranar 29 ga Mayu 1999.

Kara karanta wannan

Abubuwa 11 da Suka Taimaki Tajudden Abbas Ya Zama Shugaban Majalisar Wakilai

An kuma nada shi mataimakin shugaban majalisar dattawa a shekarar 1999, amma daga baya aka tilasta masa yin murabus.

Ya zuwa yanzu, kunji yadda Kashim Shettima ya bayyana dalilin da yasa APC ta zabi Akpabio da Abbas Tajudden su shugabancin majalisun Najeriya biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.