Jerin Kasashe Afirika 5 Da Shugaba Tinubu Ya Kulla Yarjejeniya Da Su Domin Yin Takara Da Rasha
Shugaba Bola Tinubu ya yi alƙawarin yin takara da ƙasar Rasha wajen shigar da iskar gas zuwa nahiyar Turai, inda ya ƙara da cewa bai damu da duk abinda abinda babbar ƙasar za ta ce ba.
A cikin sati uku da hawansa kan mulkin Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya fara ƙoƙarin cika wannan alƙawarin da ya ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓe.
Yadda Shugaba Tinubu ya shiga takara da Vladimir Putin na ƙasar Rasha
A ranar Juma'a, 16 ga watan Yuni ya cika kwana 19 da Shugaba Tinubu ya yi rantsuwar kama aiki, ya ƙulla yarjejeniya da wasu ƙasashen Afirika alƙalla guda biyar.
Yarjejeniyar a cewar rahoton The Punch, an yi mata laƙabi da "aikin bututun gas na $30bn tsakanin Najeriya-Morocco" sannan an rattaɓa ta ne a hedikwatar Economic Community of West African States (ECOWAS) a birnin tarayya Abuja.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Najeriya ta ƙulla yarjejeniyar ne da ƙasashen Afirika guda biyar ta hannun kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL).
Ƙasashe 5 da Shugaba Tinubu ya ƙulla yarjejeniya domin takarar da Vladimir Putin
Ƙasashen da aka ƙulla yarjejeniyar da su su ne:
1. Morocco, ta hannun Office National des Hydrocarbures et des Mines of Morocco.
2. Ivory Coast, ta hannun Société Nationale des Opérations Pétrolières of Cote d’Ivoire.
3. Liberia, ta hannun National Oil Company of Liberia.
4. Benin Republic, ta hannun Société Nationale des Hydrocarbures of Benin.
5. The Republic of Guinea, ta hannun Société Nationale des Pétroles of the Republic of Guinea.
Shugaba Tinubu ya yi alƙawarin yin takara da Rasha wajen samar da gas ga nahiyar Turai
Shugaba Tinubu a lokacin da ya yi wafa ganawa da ƴan kasuwa a Legas lokacin yaƙin neman zaɓensa ya yi kira ga ƙasashen nahiyar Turai, da su tanadi kuɗaden da za su zuɓa hannun jari wajen samar da iskar daga nahiyar Afirika, musamman Najeriya.
Bangarorin Da Tinubu Ya Kawo Sauyi
A wani labarin an yi duba kan ɓangarorin da Shugaba Tinubu ya kawo sauyi bayan ɗarewarsa kan kujerar mulkin ƙasar nan.
Tun bayan hawan Shugaba Tinubu kan shugabancin ƙasar nan, ya taɓa ɓangarori da dama daga ciki akwai ɓangaren tattalin arziƙin ƙasar nan.
Asali: Legit.ng