DSS Ta Bankado Wata Kulla-Kulla Da Ake Shiryawa Gwamnatin Tarayya Kan Tsare Emefiele, Bayanai Sun Fito

DSS Ta Bankado Wata Kulla-Kulla Da Ake Shiryawa Gwamnatin Tarayya Kan Tsare Emefiele, Bayanai Sun Fito

  • A yayin da ake ci gaba da tsare dakataccen gwamnan CBN, Godwin Emefiele, hukumar DSS tace ta gano wani shirin yi wa gwamnati ƙulle-ƙulle
  • Hukumar DSS ta fitar da wata sanarwa dangane da hakan ranar Asabar, 17 ga watan Yuni, inda ta yi nuni da cewa ba za ta bari hakan ya faru ba
  • Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa an bar Emefiele ya ga likitansa da lauyansa tun kafin kotu ta umarci a yi hakan

Abuja - Hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) ta bankaɗo wasu mutane masu shirin shirya ɓata sunan hukumar da na gwamnatin tarayya saboda dakatarwa da binciken Godwin Emefiele.

A cikin wata sanarwa ranar Asabar, 17 ga watan Yuni, da kakakin hukumar Dr. Peter Afunanya, ya fitar ya bayyana cewa mutanen sun shirya taruwa a wurare daban-daban a birnin tarayya Abuja da Legas.

Kara karanta wannan

An Zabo Mana Bala'i: Kanawa Sun Fusata Da Rushe-Rushen Abba, Sun Hana Rushe Gidajensu

DSS ta bankado kulla-kullar da ake kan Emefiele
DSS tace ta bar Emefiele ya gana da iyalansa da likita Hoto: DSS, CBN
Asali: UGC

Peter yace za su taru a wuraren ne ɗauke da alluna masu rubutu marasa kyau akan hukumar da gwamnatin tarayya tare da yin kiran a gaggauta sakin Emefiele.

Hukumar a dangane da hakan ta ja kunnen masu kitsa wannan ƙulla-ƙullar da su shiga taitayinsu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hukumar ta DSS ta kuma bayyana cewa ta bar Emefiele ya gana da iyalansa, ma'aikatan lafiya da mutanen da suka dace su ganshi tun daga ranar da ta cafke shi sannan ta samo umarnin kotu domin yin hakan.

DSS ta yi iƙirarin Emefiele ya gana da iyalansa da likitansa

Hukumar ta DSS ta kuma ƙara tabbatar da cewa Emefiele ya gana da iyalansa da likita tun kafin babbar kotun tarayya mai zamanta a Maitama-Abuja, ta bayar da umarnin a yi hakan

Hukumar DSS tace:

"Yana da kyau mu bayyana cewa mun bar iyalan Emefiele, ma'aikatan lafiya, da mutanen da suka dace su gana da shi tun daga ranar da mu ka kama shi tun kafin umarnin kotu na buƙatar aiwatar da hakan."

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kotu Ta Ba DSS Sabon Umurni a Kan Godwin Emefiele Da Ke Tsare a Hannunta

Gaskiya Ta Bayyana Kan Bidiyon Dalolin Emefiele

A wani labarin kuma, an bayyana gaskiyar zance dangane da wani bidiyon daloli da ke yawo wanda aka danganta shi da Godwin Emefiele, dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).

Binciken gaskiya ya tabbatar da bidiyon baya da wata alaƙa da Emefiele wanda yanzu haka yake garƙame a hannun DSS.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng