Tattalin Arziki Da Wasu Wurare 3 Da Tinubu Ya Kawo Sauyi Cikin Makonsa na 3 a Matsayin Shugaban Najeriya

Tattalin Arziki Da Wasu Wurare 3 Da Tinubu Ya Kawo Sauyi Cikin Makonsa na 3 a Matsayin Shugaban Najeriya

Shugaban kasa Bola Tinubu ya ci gaba da ba yan Najeriya mamaki da kuma aiwatar da manufar yakin neman zabensa na "sabonta fata" tun bayan da ya kama aiki a matsayin shugaban Najeriya a ranar 29 ga watan Mayu.

Da ake duba ayyukan shugaban kasar cikin makonsa na uku a matsayin shugaban kasar Najeriya, Tinubu ya aiwatar da manyan manufofi da matakan da suka sauya abubuwa a bangarori daban-daban na kasar.

Shugaban kasa Bola Tinubu
Tattalin Arziki Da Wasu Wurare 3 Da Tinubu Ya Kawo Sauyi Cikin Makonsa na 3 a Matsayin Shugaban Najeriya Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Wadannan manufofi da matakai sun yadu a bangarorin tattalin arziki, ilimi, rashawa da ma fannin shugabanci.

Shugaban kasa Tinubu kan tattalin arziki

Bayan dakatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) a makonsa na biyu, a cikin mako na uku sai shugaban kasa Tinubu ya umurci babban bankin da ya ba kasuwar masu saka hannun jari da masu fitarwa cin gashin kansu da kuma dakatar da farashin canji biyu.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa Tinubu Ya Karbi Bakuncin Mai Kudin Afrika, Aliko Dangote a Aso Rock

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Masana tattalin arziki da dama sun jinjinawa wannan yunkuri inda suka ce manufar zai ba masu zuba jari damar shigowa kasar kuma masana'antun cikin gida za su samu ci gaba.

Tinubu a bangaren ilimi

A ranar Litinin, 8 ga watan Yuni ne, Shugaban kasa Tinubu ya sanya hannu a dokar ba dalibai bashi, wani kudiri na da ke nufin baiwa jami’o’i da sauran manyan makarantu yancin cin gashin kansu tare da dakatar da yajin aiki a tsarin.

Yayin da wasu yan Najeriya suka yaba ma shugaban kasar, masu ruwa da tsaki ciki harda malaman ASUU da SSANU sun soki matakin na gwamnatin Tinubu.

Shugaban kasa a bangaren rashawa

Shugaban kasa Tinubu ya kuma taba yaki da rashawa da kasar ke yi lokacin da ya dakatar da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Abdulrasheed Bawa.

Kara karanta wannan

Muhammadu Sanusi II Ya Fayyace Dalilan Zuwa Aso Rock da Abin da Ya Fadawa Tinubu

An kuma bukaci Bawa da ya mika shugabanci ga mataimakinsa sannan ya gabatar da kansa don bincike a jerin zarge-zargen da ake yi masa.

Tinubu ya tabo bangaren gwamnati

Shugaban kasar Najeriyan ya kuma tabo bangaren gwamnati inda ya nada masu bayar da shawara na musamman guda takwas a ranar Alhamis, 15 ga watan Yuni.

Cikin wadanda ya nada harda shugaban EFCC na farko, Nuhu Ribadu; tsoffin kwamishinoninsa biyu a lokacin da yake gwamnan jihar Lagas, Dele Alake da Wale Edun; tsohon ma'aikacin marigayi tsohon gwamna Abiola Ajimobi na jihar Oyo, Zacchaeus Adedeji da wasu biyar.

"A duba lamarinmu": Yan Abuja sun roki shugaban kasa Tinubu da ya basu minsitan Abuja

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa yan asalin Abuja sun mika kokon bararsu a gaban shugaban kasa Bola Tinubu inda suka roki ya basu kujerar ministan babban birnin tarayya.

Yan asalin yankin wadanda suka ce an dade ana cutarsu sun ce babu yadda za a yi a ci gaba da dauko masu bakin haure domin jibantar lamuransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng