“Allah Ka Albarkaci Nemana”: Bidiyo Ya Hasko Kyakkyawar Budurwa Tana Tuwon Siyarwa

“Allah Ka Albarkaci Nemana”: Bidiyo Ya Hasko Kyakkyawar Budurwa Tana Tuwon Siyarwa

  • An gano wata matashiya yar Najeriya wacce ke siyar da tuwon rogo tana hada abincin domin kaiwa kasuwa
  • Matashiyar tana da tsananin kyau da ya sa mutane da dama garzaya sashin sharhi na bidiyon don yaba haduwarta
  • Ta roki Allah ya albarkaci ayyukan hannunta, kuma mutane da dama sun taya ta addu'a sannan sun bukaci ta ci gaba da aiki tukuru

Wata matashiya ta garzaya dandalin TikTok don nunawa mutane abun da take yi don dogaro da kai kuma bidiyon ya yadu.

Matashiyar mai suna Nelly Promise a TikTok ta gazaya dandalin don nunawa duniya cewa tuwo take siyarwa don dogaro da kai.

Matashiya na hada tuwon siyarwa
“Allah Ka Albarkaci Nemana”: Bidiyo Ya Hasko Kyakkyawar Budurwa Tana Tuwon Siyarwa Hoto: TikTok/@nellypromise4
Asali: TikTok

A bidiyon, Nelly ta fara aikin harhada kullunta a katon baho sannan ta kulla kafin ta daura rusheshen tukunya a wuta.

Da ta kammala dafa tuwon, sai ta daka shi da kyau ya yi sumul-sumul kafin ta daddaura shi a leda don siyarwa.

Kara karanta wannan

"Ya Yi Bulokin Dina": Budurwa Ta Koka Bayan Saurayinta Ya Dandana Abincinta Ya Tsere, Ta Tambayi Dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matashiya ta burge mutane da jajircewarta a sana'arta na tuwo

Yanayin yadda ta aiwatar da aikin gaba daya ya burge mabiyanta a dandalin TikTok.

Baya ga kwazon aiki da Nelly ke da shi, wani abu da ya kara jan hankalin mutane zuwa ga bidiyon shine tsananin kyawun da take da shi.

Ta rubuta a jikin bidiyon:

"Ya Allah, nagode da wannan damar gudanar da wannan kasuwanci. Na yarda da hikimarka yayin da nake neman aiki tukuru don kare shi da yin nasara. Da fatan kyawawan ayyukana su zama ginshikin duk abin da nake yi."

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@nnamdi751 ya ce:

"Shin Hilda ta dafa Fufu a wannan ranar na 4? Ko dai Indomie da shinkafa take girkawa?"

@oscar_moni_ ya yi martani:

"Ina kaunarki yar'uwa."

@alamanjohope ya ce:

"Allah ya albarkaci aikin hannunki."

Kara karanta wannan

“Sadakina Ya Karu”: Matashiya Ta Dafa Kwai Karo Na Farko A Rayuwarta, Ya Fito Kamar Bayan Tukunya a Bidiyo

@ritaeewa4xd ya yi martani:

"Allah ya albarkace ki. Ina maki addu'an samun karin kwastamomi da sunan Allah na yi addu'a."

@Victoria Charles ta ce:

"Sannu da aiki. Akwai riba a aiki tukuru."

Matashiya ta dafa kwai karo na farko a rayuwarta, ya babbake kamar bayan tukunya

A wani labari na daban, mun ji cewa wata matashiya yar masu hannu da shuni ta yi kokarin dafa kwai karo na farko a rayuwarta, amma sai aka yi rashin dace domin dai kwan ya babbake fiye da tunani.

Rike da konannen kwai a hannunta, matashiyar cike da barkwanci ta bayyana yadda ake dafa irin kwanta: "Kawai ka zuba ruwa a kan wuta, sai ka saka kwan a ciki, sannan ka yi bacci."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng