Dan Sandan Da Ya Dawo Da $800 Na Wata Hajiya a Katsina, Ya Samu Kyautar Kujerar Aikin Hajji

Dan Sandan Da Ya Dawo Da $800 Na Wata Hajiya a Katsina, Ya Samu Kyautar Kujerar Aikin Hajji

  • Nura Mande, ɗan sandan da ya mayar da ɗaruruwan daloli ga wata hajiya, ya samu kyauta mai tsoka bisa kishin da ya nuna
  • An ba Mande kyautar tikitin zuwa aikin hajjin bana na shekarar 2023 a ƙasa mai tsarki domin ya je ya sauke farali
  • Ɗan sandan dai ya yi wannan aikin kirkin ne a shekarar 2022 lokacin da wata tsohuwa, Hajiya Hadiza Usman, ta yarda kuɗinta waɗanda Mande ya tsinta

Jihar Katsina - Konstabul Nura Mande, ɗan sandan da ya tsinci kuma ya mayar da $800 na kuɗin guzurin wata hajiya daga jihar Katsina a shekarar 2022, ya samu kyautar zuwa ƙasa mai tsarki domin gudanar da hajjin bana na shekarar 2023.

A cewar rahoton Daily Nigerian, hakan ya bayyana ne a ranar Juma'a, 16 ga watan Yuni, a cikin wata sanarwa da CSP Gambo Isah, kakakin rundunar ƴan sanda shiyya ta 14 a jihar Katsina, ya fitar.

Kara karanta wannan

An Maka Budurwa A Kotu Kan Sama Da Fadi Da Naira Miliyan 4 Da Ƙawarta Ta Ba Ta Ajiya A Abuja

An kai dan sandan da ya dawo da kudi aikin Hajji
Kakakin ya ce kudaden na wata tsohuwa ce Hoto: Dailynigerian.com
Asali: UGC

A cikin sanarwar, kuɗaɗen da aka dawo da su mallakin Hajiya Hadiza Usman ne, wata tsohuwa daga ƙaramar hukumar Kusada ta jihar Katsina.

Sai dai, sanarwar ba ta bayyana sunan mutumin da ya bayar da kyautar kujerar hajjin ga ɗan sandan ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mr Isah ya bayyana cewa mutumin da ya yi alƙwarin ba ɗan sandan kyautar zuwa aikin Hajji na shekarar 2023, ya cika alƙawarin da ya ɗauka.

Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta karrama Mande bisa kwazon da ya nuna

"Yanzu haka da na ke magana da ku, Nura Mande yana ƙasa mai tsarki domin gudanar da Hajjin bana na wannan shekarar." A cewarsa
"Muna godiya ga Allah da mutanen jihar Katsina bisa addu'o'insu, kyaututtukansu da nuna goyon bayansu ga jami'an ƴan sanda."

Ɗan sanda har takardar yabo ya samu daga kwamishinan ƴan sandan jihar, bisa ɗaga darajar rundunar ƴan sanda.

Kara karanta wannan

Abdulsamad Rabiu Ya Rasa Sama Da N1trn a Dukiyarsa Cikin 'Yan Sa'o'i, Ya Yo Kasa a Jerin Attajiran Duniya

Gwamna Uzodimma Ya Daukin Nauyin Mahajjata 200

A wani labarin, gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya ɗauki nauyin mahajjata 200 domin zuwa ƙasa mai tsarki su gudanar da aikin hajji.

Wannan shi ne dai karo na farko a cikin shekara 10 da wani gwamna a jihar da ke a yankin Kudu maso Gabashin ƙasar nan, ya aiwatar da hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng