Hotuna Sun Yadu Yayin da Tinubu Ya Karbi Bakuncin Dangote a Aso Rock, Jama’a Sun Yi Martani
- Shugaban kasa Bola Tinubu ya gana da mai kudin Afrika, Aliko Dangote a fadar shugaban kasa, Abuja
- Shugabannin sun yi kus-kus a tsakaninsu a yau Juma'a, 16 ga watan Yuni, amma babu cikakken bayani kan ganawar tasu zuwa yanzu
- Yan Najeriya sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyanan hotunan jiga-jigan kasar biyu a soshiyal midiya
Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya karbi bakuncin mai kudin Afrika, Alhaji Aliko Dangote a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Juma'a, 16 ga watan Yuni.
Dangote ya shiga jerin manyan masu ruwa da tsakin da suka zaiyarci Shugaban kasa Tinubu tun bayan da ya hau karagar mulki a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sai dai kuma, ba a tabbatar da abun da ganawar tasu ta kunsa ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton amma akwai alamu da ke nuna kawai ziyarar ban girma ce ko kuma dai jiga-jigan kasar biyu sun tattauna ne game da yiwuwar hada kai don bunkasa tattalin arzikin Najeriya.
An gano manyan mutanen biyu tare a cikin wani hoto da ya yadu a soshiyal midiya inda mutane suka tofa albarkacin bakunansu kan ganawar tasu.
Jama'a sun yi martani
@Ara_tunji ya tambaya:
“Shin da gaske ne cewa an ba shi lasisi a matsayin shi kadai ne zai dunga shigo da man fetur? Idan da gaske ne, to mene ne amfanin murnar cire tallafin mai?”
@_mai_daraja ya yi martani:
"Kudi da kudi da mulki ."
@KymmoAkeem ya yi martani:
"Na yi tunanin wannan ziyarar awanni 24 da suka wuce. Emefiele da Dangote na da tambayoyin da za su amsa."
@ajindeh ya ce:
Bayan Ganawa da Tinubu, Asri Dakubo Ya Tona Asirin Wasu Sojoji Da Ke Ɗaukar Nauyin Ɓarayin Mai a Najeriya
"Dangote ya fara kamun kafa kuma, ologbon sodiq "
@Abraham96853055 ya ce:
"Mutumin da ya fi kowa mugunta a duniya .. ya janye komai… yana son ya zama mai arziki shi kadai ta hanyar gwamnati.. yanzu yana son ya yi kane-kane kan man fetur.. wannan mugunta ne.”
Shugaban kasa Tinubu ya gana da Asari Dokubo
Mun ji a baya cewa Bola Ahmed Tinubu ya gana da tsohon ɗan tawaye a yankin Neja Delta, Asari Dokubo, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Dakubo ya isa fadar shugaban ƙasa da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar ranar Jumu'a kuma daga zuwa ya shiga ganawar sirri da shugaba Tinubu.
Asali: Legit.ng