Yanzu Yanzu: Kotu Ta Umurci DSS Ta Gaggauta Ba Emefiele Damar Ganin Lauyoyi Da Iyalinsa

Yanzu Yanzu: Kotu Ta Umurci DSS Ta Gaggauta Ba Emefiele Damar Ganin Lauyoyi Da Iyalinsa

  • Babbar kotun tarayya da ke zama a Maitama Abuja ta ba hukumar DSS umurnin ba dakataccen gwamnan CBN damar ganawa da lauyoyi da iyalinsa
  • Godwin Emefiele na tsare a hannun hukumar tsaro ta farin kaya tun bayan dakatar da shi da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi
  • Justis Hamza Muazu ya ce Emefiele na da yancin ganin lauyoyi da iyalinsa kamar yadda yake a kundin tsari

Abuja - An umurci Darakta Janar na hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da DSS da su gaggauta ba dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, damar ganawa da lauyoyi da iyalinsa domin haka yana bisa yancinsa.

Jami'an DSS sun kama Emefiele jim kadan bayan shugaban kasa Bola Tinubu ya dakkatar da shi a daren ranar Juma'a.

Dakataccen gwamnan CBN, Godwin Emefiele
Yanzu Yanzu: Kotu Ta Umurci DSS Ta Gaggauta Ba Emefiele Damar Ganin Lauyoyi Da Iyalinsa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Justis Hamza Muazu na babbar kotun tarayya da ke zama a Maitama Abuja ne ya bayar da umurnin a ranar Juma'a, 16 ga watan Yuni bayan J. B. Daudu SAN, lauyan Emefiele ya shigar da wata bukata, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

DSS Ta Gano Tarin Kudi a Gidan Emefiele? Gaskiya Ta Bayyana

Ya sanar da kotun cewa ya rubuta wasiku ga DSS, musamman a ranar 14 ga watan Yuni, domin neman karin umarni daga wajensa, amma DSS ta ki amsa bukatar, rahoton Daily Post.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

DSS za ta bi umurnin kotu, lauya

A daya bangaren, lauyan wadanda ake kara na biyu da na uku, I. Awo, ya shaida wa kotun cewa hukumar DSS ba ta da hurumin kin amincewa da wannan bukata, kuma cewa yin hakan ba daidai ba ne.

Saboda haka, ya nuna yakinin cewa hukumar tsaron za ta bi umurnin kotu sannan za ta ba jerin lauyoyi da dangin Emefiele damar ganinsa, yayin da lauyan ofishin Atoni Janar na tarayya bai yi adawa da bukatar ba.

DSS ta yi watsi da bidiyon da ke alakanta Emefiele da wani tarin kudi da aka gano

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Bayyana Kan Halin da Dakataccen Gwamnan CBN Ke Ciki Kwana 6 a Hannun DSS

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani bidiyo ya bayyana a soshiyal midiya yana nuno wasu tarin kudade da ake zargin an gano su ne a cikin gidan Godwin Emefiele, dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).

Wani bincike da jaridar The Cable ta gudanar kan bidiyon da ya yadu ta gano daga kasar Sudan ya fito. An kuma dauki bidiyon ne tun a ranar 22 ga watan Afrilun 2019, lokacin da aka gano damin tsabar kudi da ya kai sama da dala miliyan 7 a gidan Omar Bashir.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng