Binciken Kwakwaf: Bidiyon Tarin Dala Da Aka Danganta Da Emefiele Ba Daga Najeriya Bane

Binciken Kwakwaf: Bidiyon Tarin Dala Da Aka Danganta Da Emefiele Ba Daga Najeriya Bane

  • Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele na tsare a hannun rundunar yan sandan farin kaya (DSS)
  • Yan kwanaki bayan nan, wani bidiyo ya yadu a soshiyal midiya, yana ikirarin cewa an gano tarin kudade a gidan Emefiele bayan kama shi
  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Emefiele a ranar Juma, 9 ga watan Yuni, saboda binciken da ake yi a ofishinsa

Wani bidiyo ya bayyana a soshiyal midiya yana nuno wasu tarin kudade da ake zargin an gano su ne a cikin gidan Godwin Emefiele, dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).

A bidiyon mai tsawon sakan 26, an gano wasu maza biyu suna kirga makudan kudade na daloli da wata na'ura.

Wani rubutu da ya biyo bayan bidiyon ya yi ikirarin cewa gidan da aka gano kudin mallakin Emefiele ne.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kotu Ta Ba DSS Sabon Umurni a Kan Godwin Emefiele Da Ke Tsare a Hannunta

Damin kudi da Emefiele
Binciken Kwakwaf: Bidiyon Tarin Dala Da Aka Danganta Da Emefiele Ba Daga Najeriya Bane Hoto: @akerele_s, @cenbank
Asali: Twitter

Legit.ng ta lura cewa yawancin masu amfani da soshiyal midiya da suka yada bidiyon masu biyayya ga shugaban kasa Bola Tinubu ne - kamar yadda aka gani a nan da nan. Haka kuma bidiyon bidiyon da ke nuna dalolin baya dauke da sautin murya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tun a 2022 ne DSS ke kula da duk wani motsin Emefiele kan zargin daukar nauyin ta'addanci, zargi da ya karyata da babban murya.

Jim kadan bayan shugaban kasa Bola Tinubu ya sanar da dakatar da Emefiele a matsayin gwamnan CBN a ranar Juma'a, sai rahotanni suka kawo cewa jami'an DSS sun kama shi.

Bayan an kai ruwa rana, DSS ta fito a ranar Asabar inda ta ce Emefiele na a hannunta saboda wasu bincike da take gudanarwa.

Yan awanni bayan nan, sai aka gano wani bidiyo yana yawo a dandalin soshiyal midiya, inda yake ikirarin cewa an gano kudade a gidan Emefiele bayan kama shi, jaridar The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Bayyana Kan Halin da Dakataccen Gwamnan CBN Ke Ciki Kwana 6 a Hannun DSS

Bidiyon tsoho ne kuma daga kasar Sudan ya fito

Wani bincike da jaridar The Cable ta gudanar kan bidiyon da ya yadu ta gano daga kasar Sudan ya fito.

An dai gano cewa an dauki bidiyon ne tun a ranar 22 ga watanAfrilun 2019, lokacin da aka gano damin tsabar kudi da ya kai sama da dala miliyan 7 a gidan Omar Bashir, tsohon shugaban kasar Sudan.

Bashir ya kasance tsohon jami'in sojan kasar Sudan kuma dan siyasa wanda ya yi aiki a matsayin shugaban kasar Sudan na bakwai bisa mukamai daban-daban daga 1989 zuwa 2019 lokacin da aka hambarar da shi.

DSS ta yi martani ga bidiyon

Da ata tuntube shi don ji ta bakinsa, Peter Afunaya, kakakin rundunar tsaron farin kaya (DSS), ya bayyana cewa bidiyon na bogi ne.

Tinubu ya dakatar da gwamnan CBN, Godwin Emefiele

A wani labari makamancin wannan, mun ji a baya cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban CBN.

Tinubu ya dakatar da Emefiele daga kujerarsa ne a ranar Juma'a, 9 ga watan Yuni, har zuwa lokacin da za a kammala bincike a kujerarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng