NAHCON: Yadda Maniyyata Mata 75 Suka Kare a Asibitin Makkah da Madina

NAHCON: Yadda Maniyyata Mata 75 Suka Kare a Asibitin Makkah da Madina

  • Hukumar NAHCON ta bayyana yadda wasu maniyyata akalla 75 suka ƙare a Asibitocin Makkah da Madina daga zuwa aikin Hajjin bana
  • Jami'in tawagar likitocin Najeriya ya ce mafi akasarin maniyyata mata masu ciki sun yi fatali da gargaɗin da NAHCON ta musu tun a gida
  • Ya ce sun tura maniyyata mata masu juna biyu 30 Asibiti a Madina, yayin da wasu 45 aka kwantar da su a Makkah

Hukumar kula da alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta bayyana cewa kawo yanzu an kwantar da maniyyata mata 75 masu ɗauke da juna biyu a asibitocin Makkah da Madina.

Jaridar Punch ta rahoto ce an garzaya da maniyyatan masu ciki Asibiti ne domin kula da lafiyarsu sakamakon abinda su ke ɗauke da shi kuma ga aikin Hajji.

Masu zuwa aikin Hajji.
NAHCON: Yadda Maniyyata Mata 75 Suka Kare a Asibitin Makkah da Madina Hoto: NAHCON
Asali: Depositphotos

NAHCON ta ce mafi yawan maniyyata sun sa kafa sun shure shawarwari da kuma wayar da kan da aka musu kan cewa duk mace mai juna biyu ta haƙura da tafiya aikin Hajjin bana.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bala'i Ya Auku Yayin Da Yan APC Suka Mutu A Hadarin Mota A Hanyar Zuwa Abuja

Usman Galadima, jami'in da ke aiki a tawagar Likitocin Najeriya a Makkah ne ya bayyana haka yayin wata hira da yan jarida ranar Laraba, 14 ga watan Yuni, 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce tun da fari hukumar ta gargaɗi mata masu juna biyu su guji tafiya aikin hajji saboda wahalar aikin da kuma ɗawainiyar da ke ciki.

Ya kuma ƙara da bayanin cewa daga cikin masu juna biyu 75 da aka kwantar kawo yanzu, 30 daga ciki suna kwance a Asibitin Madinah yayin da sauran 45 aka kai su Asibitin Makkah.

Tun farko mun ba da shawarwari amma suka ƙi ji - NAHCON

A ruwayar Premium Times, ya ce:

"Mun haɗu da Kes din masu tsohon ciki. Mun ga masu juna biyu na tsawon watanni 7 da ya zama wajibi a kwantar da su. Muna da waɗanda aka kai Asibitin Mata a Makkah domin ba su kulawar gaggawa."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kashe Rai, Sun Yi Garkuwa da Sarakuna 2 a Jihar Bauchi

"Wannan ya faru ne duk da gargaɗin da muka yi wa mata masu ciki kar su yi kuskuren tahowa ƙasa mai tsarki a halin da suke ciki saboda hangen abinda ka iya biyo baya."
"Mun ba da shawara tun farko, kada mace mai ciki ta zo aikin Hajji, duk da haka mun samu masu cikin da suka taho Hajjin bana. A Madina mun kai maniyyata masu ciki 30 Asibiti, mun tura wasu 45 a Makkah."

Shugaba Tinubu Ya Nada Ribadu, Darazo, Alake da Wasu 5 a Matsayin Mashawarta

A wani rahoton na daban kuma Shugaban Najeriya, Alhaji Bola Ahmed Tinubu, ya amince da naɗa mutane 8 a matsayin ma su ba da shawara.

A wata sanarwa da ta fito daga fadar shugaban ƙasa, Tinubu ya naɗa Nuhu Ribaɗo, Ya'u Darazo da wasu jiga-jigai a muƙamai daban-daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262