An Shiga Jimami Yayin Da Babban Basarake A Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Babban basarake, Oba Saburee Babajide Isola Bakre, Jamolu II na Gbagura, a Egbaland, ya riga mu gidan gaskiya
- Babban basaraken, Agura na Gbagura, ya rasu ne a ranar Laraba, 14 ga watan Yuni, a wani asibiti wanda ba a bayyana ba
- Rasuwar basaraken an bayyana ta ne a cikin wata sanarwa da Osi na Egbaland da Balogun na Ibadan Gbagura a Abeokuta suka fitar
Jihar Ogun - Babban basarake a jihar Ogun, Oba Saburee Babajide Isola Bakre, Jamolu II na Gbagura, Egbaland, a Abeokuta, ya riga mu gidan gaskiya.
A cewar rahoton Nigerian Tribune, marigayin basaraken, wanda shi ne Agura na tara a Gbagura, ya rasu ne a ranar Laraba, 14 ga watan Yuni.
An tattaro cewa basaraken ya fara rashin lafiya ne ranar Talata da rana inda aka kai shi wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba a birnin Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Basaraken ya rasu ne a asibiti
Daga nan an sake tura basaraken zuwa wani asibiti a jihar Legas a ranar ta Talata domin ci gaba da duba lafiyarsa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Osi na Egbaland da Balogun na Ibadan Gbagura a Abeokuta, ta hannun Cif Rasaq Adesola Obe, Balogun Ijayekukudi da sakataren fadar Agura, su ne suka sanar da rasuwar basaraken cikin wata sanarwa a safiyar ranar Alhamis, 15 ga watan Yuni.
Sanarwar na cewa:
Mai martaba Osi na Egbaland da Balogun na garin Ibadan Gbagura a Abeokuta ya umarce ni da na sanar da ku cewa mai martaba, Oba Dr Saburee Babajide Bakre Jamolu 11, Agura na Gbagura, ya koma ga mahaliccinsa a ranar Laraba, 14 ga watan Yunin 2023."
"Allah ya jiƙan Kabiyesi da rahama. Allah ya ba iyalansa, ƴan majalisar sarkin Gbagura, haƙurin jure wannan gagarumin rashi da aka yi."
Babban Basarake Mai Shekara 87 Ya Kwanta Dama
A wani labarin na daban kuma, babban basarake mai sarautar Babban basarake mai sarautar Onidimu na ƙasar Idimu, Oba Azeez Dada Aluko Olugoke, ya koma ya yi bankwana da duniya yana da shekara 87.
Basaraken ya bar duniya ne bayan ya yi fama da ƴar gajeruwar rashin lafiya kamar yadda hukumomi suka bayyana a sanarwar da suka fitar kan mutuwarsa.
Asali: Legit.ng