Abubuwa 4 Da Ake Ganin Suna Da Alaka Da Dakatar Da Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa Da Tinubu Ya Yi
Da yammacin ranar Laraba 14 ga watan Yuni ne, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya ba da umarnin dakatar da shugaban Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa (EFCC), Abdulrasheed Bawa.
Sanarwar wacce daraktan yaɗa labarai na ofishin sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey ya sanyawa hannu, ta ce an dakatar da Bawa ne saboda a samu damar gudanar da sahihin bincike a kansa.
Dakatarwar ta Abdulrasheed Bawa na zuwa ne cikin abinda bai wuce mako guda ba da Shugaba Tinubu ya dakatar da gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
Mun tattaro muku daga wani rahoto da Daily Trust ta wallafa, wasu abubuwa guda huɗu da suke da alaƙa da dakatarwar da aka yi wa Abdulrasheed Bawa daga EFCC.
1. Rawar da Bawa ya taka kan batun sauya fasalin kuɗi
Wasu dai na ganin cewa Shugaba Tinubu da makusantansa, ba su ji daɗin irin rawar da dakataccen shugaban na EFCC ya taka ba a lokacin da aka zo da batun sauya fasalin kuɗi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk da cewa babban bankin Najeriya (CBN), ya bayyana cewa saboda magance hauhawar farashi ya sauya fasalin, Shugaba Tinubu da makusantansa na ganin cewa kawai an yi hakan ne domin yaƙar takarar da yake a lokacin.
Bawa ya taɓa bayyana cewa akwai 'yan siyasa da dama da suka jibge kuɗaɗen haram a wajensu, amma tsarin sauya fasalin kuɗin zai taimaka wajen bankaɗo su.
2. Takun saƙarsa da Bello Matawalle
A kwanakin baya ne Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa (EFCC), ta ce ta aikawa tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle da takardar bincike kan badaƙalar kuɗi da suke tuhumarsa da ita.
Sai dai a nasa martanin, Bello Matawalle ya yi iƙirarin cewa Abdulrasheed Bawa na EFCC, ya taɓa neman ya bashi cin hancin dala miliyan biyu ($2m), zargin da Bawan ya musanta.
3. Kiraye-kirayen ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam
A kwanakin baya, an samu wasu ƙungiyoyin da ke fafutukar kare haƙƙin ɗan adam da suka nemi a dakatar da Abdulrasheed Bawa daga shugabancin na EFCC.
Ƙungiyoyin sun zargi Bawa da siyasantar da ayyukan binciken da Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa (EFCC) ke gudanarwa na zaɓar waɗanda hukumar ke son ta tuhuma.
Sai dai hukumar ta a EFCC ta yi wa masu kiraye-kirayen martani, inda ta ce zargin da suke yi ba shi da tushe ko makama.
4. Canjin Gwamnati da alaƙakrsa da Malami
Wasu na ganin cewa a duk lokacin da aka samu sauyin shugabancin ƙasa, akan samu sauyin shugabanci a hukumar ta EFCC ko da kuwa babu dalilin hakan.
Da Dumi-Dumi: Shugaban Kasa Tinubu Ya Dakatar Da Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa, Har Sai Baba-Ta-Gani
Mallam Auwal Musa Rafsanjani, wani mai fafutukar ɗabbaƙa doka da oda ya bayyana cewa, dakatar da aka yi wa Bawa ba za ta rasa nasaba da alaƙarsa da tsohon ministan shari'a Abubakar Malami ba, wanda kuma ake ganin ba shi da wata kyakkyawar alaƙa da Shugaba Tinubu.
EFCC ta gayyaci ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika
A wani labarin da Legit.ng ta kawo muku a baya, kun karanta cewa Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa (EFCC), ta gayyaci tsohon ministan sufurin jiragen sama ƙarƙashin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Hadi Sirika don amsa tambayoyi.
Hukumar dai ta yi wa Hadi Sirika tambayoyi ne dangane da batun jirgin saman 'Nigerian Air' da ake ta kace nace akansa.
Asali: Legit.ng