EFCC Ta Gayyaci Tsohon Ministan Buhari, Sirika, Ta Yi Wa Jami’an Kamfanin Jirgin Najeriya Tambayoyi
- Hukumar EFCC ta gayyaci Hadi Sirika, tsohon ministan sufurin jiragen sama karkashin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari don amsa tambayoyi
- An gayyaci Sirika domin ya amsa tambayoyi kan takkadamar da ke kewaye da naira biliyan 80 da ake zargin ya kashe wajen kaddamar da jirgin Najeriya yan kwanaki kafin barin ofis
- Tsohon ministan shine mutum na biyu da hukumar yaki da rashawar ke bincika a majalisar Buhari cikin kwanaki 20 da barin ofis
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gayyaci tsohon ministan sufurin jiragen sama karkashin tsohuwar gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hadi Sirika, don amsa tambayoyi.
A cewar jaridar This Day, hukumar ta yi wa jami'an kamfanin jirgin saman Najeriya tambayoyi kan aikin kaddamar da jirgin da tsohon ministan ya yi a kuraren lokaci a Abuja.
Dalilin da yasa EFCC ta gayyaci Hadi Sirika, tsohon ministan Buhari
Ana sa ran tsohon ministan zai gurfana a gaban hukumar yaki da rashawar cikin makon nan don amsa tambayoyi dangane da kaddamar da jirgin saman Najeriyan da aka kawata da kalar Habasha.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wilson Uwujaren, kakakin hukumar EFCC, ya tabbatar da ci gaban, cewa ana gudanar da bincike amma ba zai bayar da cikakken bayani ba.
Uwujaren ya ce:
"Zan iya tabbatar da cewar ana gudanar da bincike a kan haka."
EFCC na binciken biliyan N3 da aka zuba a jirgin saman Najeriya
Majiyoyi cikin hukumar sun kuma bayyana cewa hukumar za ta binciki naira biliyan 3 da aka zuba a aikin jirgin saman Najeriya koda dai wasu masun ruwa da tsaki sun sha zargin cewa fiye da miliyan 80 aka kashe a aikin.
Da Dumi-Dumi: Shugaban Kasa Tinubu Ya Dakatar Da Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa, Har Sai Baba-Ta-Gani
Yan kwanaki kafin karewa gwamnarin Buhari, Sirika ya sanar da kaddamar da kamfanin jirgin saman Najeriya ta hanyar amfani da jirgin saman Habasha.
Wannan ci gaban ya kara baiwa masu ruwa da tsaki takaici, inda suka yi zargin cewa jirgin saman na Habasha ya isa Najeriya dauke da kalar kasar Habashan, suna masu cewa hakan bai dace ba ko kadan a matsayin jirgin na kasa.
Sirika shine tsohon ministan gwamnatin Buhari na biyu da EFCC za ta bincika. Da farko hukumar yaki da rashawar ta gayyaci Pauline Tallen, tsohuwar ministar harkokin mata.
EFCC ta tsitsiye tsohuwar ministar Buhari, Pauline
Legit.ng ta kawo a baya cewa, EFCC ta tsitsiye tsohuwar ministar harkokin mata, Pauline Tallen, kan zarginta da aikata rashawa.
An tattaro cewa Tallen ta isa ofishin hukumar na Abuja a ranar Alhamis, 1 ga watan Yuni domin amsa tambayoyi kan karkatar da kudi naira biliyan 2.
Asali: Legit.ng