Abdulrasheed Bawa, Dakataccen Shugaban EFCC, Ya Isa Ofishin DSS Don Amsa Tambayoyi
2 - tsawon mintuna
- Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Abdulrasheed Bawa, shugaban Hukumar Yaki da Rashawa da Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa, EFCC, a ranar Laraba, 14 ga watan Yuni kan zargin aikata ba dai-dai ba
- Tinubu ya bayyana dakatarwar cikin wata takarda da darektan watsa labarai na ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey, ya fitar
- Bayan yan awanni da dakatarwar, Hukumar Yan Sandan Farin Kaya, DSS, ta gayyaci dakataccen shugaban na EFCC, Abdulrasheed Bawa domin zurfafa bincike
Hukumar Yan Sandan Farin Kaya, DSS, a daren ranar Laraba, ta ce ta gayyaci dakataccen Shugaban Hukumar Yaki da Rashawa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, don zurfafa bincike.
Mai magana da yawun DSS Peter Afunaya, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Laraba a Twitter.
Abin da ya sa DSS ta gayyaci Abdulrasheed Bawa, dakataccen shugaban EFCC
An gayyaci Bawa ne bayan dakatarwar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi masa na sai baba-ta-gani 'don bada damar yin sahihin bincike kan ayyukansa yayin da ya ke ofis'.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sanarwar da Legit.ng Hausa ta gani ya ce:
"Hukumar Yan Sandan Farin Kaya, DSS, ta gayyaci Abdulrasheed Bawa, dakataccen Shugaban Hukumar Yaki da Rashawa ta Yi Wa Tattalin Arziki Zagon Kasa, Bawa, ya iso yan awanni da suka gabata.
"Gayyatar da aka masa na da alaka da binciken da aka yi a kansa.
"Peter Afunanya, Jami'in Hulda da Al'umma, Hukumar Yan Sandan Farin Kaya, Hedkwatar Kasa na Abuja, ya tabbatar da hakan a daren ranar Laraba, 14 ga watan Yunin 2023."
Asali: Legit.ng