Mohammed Umar Abba: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Shugaban Riko Na EFCC Bayan Magu
- Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya sanar da dakatarwar da ya yi wa shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (EFCC), AbdulRasheed Bawa, har illa ma sha Allahu
- Mohammed Umar Abba, kwamishinan 'yan sanda, shi ne ya karɓi Magu a matsayin shugaban riko na hukumar ta EFCC jim kaɗan bayan dakatar da shi
- A lokacin da aka dakatar da Magu, Abba shi ne ke riƙe da mafi ƙololuwar muƙami a hukumar, wato muƙamin daraktan ayyuka, wanda yake a kai tun shekarar 2017
A ranar Larabar ne shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya dakatar da shugaban Hukumar Yaƙi da Masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), AbdulRasheed Bawa bisa wasu manyan zarge-zarge da ke da alaƙa da ofishinsa.
A cewar wata sanarwa da ofishin sakataren Gwamnatin Tarayya ya fitar, an dakatar da Bawa ne don gudanar da sahihin bincike kan yadda ya gudanar da ayyukansa a lokacin da yake kan mukaminsa, in ji rahoton Vanguard.
Dalilin dakatar da Abdulrashid Bawa a matsayin shugaban EFCC
Dakatarwar ba za ta rasa nasaba da wasu zarge-zarge masu nauyi da wasu masu ruwa da tsaki a yaƙi da cin hanci da rashawa suka yi masa ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Bayan dakatarwar da aka yi masa, an umarci Bawa da ya gaggauta miƙa al’amuran ofishinsa ga daraktan ayyuka na hukumar, wanda zai kula da harkokin ofishin shugaban na EFCC.
Umarnin da shugaban ƙasa ya bayar ya haifar da ruɗani, inda wasu rahotanni ke nuni da cewa Mohammed Umar Abba shi ne daraktan ayyuka kuma zai karbi ragamar mulki daga hannun Bawa.
Sai dai wata sanarwa da hukumar ta EFCC ta fitar (a ranar 28 ga Mayu, 2023), ta nuna cewa Abdulkarim Chukkol, shi ne daraktan ayyuka ba Abba ba.
Wannan yana nuni da cewa Bawa zai mika wa Chukkol ne ba Abba ba, kamar yadda aka ruwaito a baya.
Duk da haka, Legit.ng ta binciko cewa, Abba ya taba riƙe muƙamin shugaban riƙo na EFCC. Ya shugabanci hukumar ne biyo bayan dakatarwar da aka yi wa Ibrahim Magu (tsohon shugaban EFCC) a ranar 6 ga Yuli, 2020.
Watanni bakwai bayan haka, Abba ya mikawa shugaban hukumar, Abdulrasheed Bawa, a ranar 24 ga Fabrairu, 2021.
Ga duk abin da kuke buƙatar sani game da tsohon shugaban hukumar EFCC na riƙo:
Mohammed Umar Abba, mai muƙamin kwamishinan ‘yan sanda (CP), a ranar 9 ga Yulin shekarar 2020, ya zama shugaban riƙo na hukumar ta EFCC, saboda kasancewarsa babban jami’in gudanarwa na hukumar.
Hakan a lokacin ya biyo bayan dakatar da Magu da aka yi a ranar 6 ga Yuli, 2020. Bayan watanni bakwai, Abba ya miƙa shugabancin hukumar ga Abdulrasheed Bawa, a ranar 24 ga watan Fabrairu, 2021.
Da Dumi-Dumi: Shugaban Kasa Tinubu Ya Dakatar Da Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa, Har Sai Baba-Ta-Gani
An haife Abba a ranar 22 ga watan Yunin 1965 a karamar hukumar Tudunwada ta jihar Kano, Abba ya yi digirinsa na farko a jami’ar Bayero da ke Kano.
Shigar Mohammed Umar Abba aikin ɗan sanda da EFCC
Bayan kammala digiri, Abba ya yi aikin bautar ƙasa na shekara ɗaya a tsohuwar hukumar rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, inda daga bisani ya shiga aikin ‘yan sandan Najeriya.
Ya halarci makarantar horas da ‘yan sanda ta jihar Kaduna, inda ya fara aiki a shekarar 1992.
Abba ya shigo hukumar EFCC ne a watan Janairun 2016, domin ya jagoranci ɓangaren yaƙi da ta’addanci da bincike a hedikwatar hukumar da ke Abuja.
An naɗa shi daraktan ayyuka na hukumar a shekarar 2017, inda ya rike har zuwa 2020 lokacin da ya karɓi ragamar shugabancin hukumar daga Ibrahim Magu a matsayin shugaban riko.
Tinubu ya dakatar da gwamnan babban bankin Najeriya (CBN)
Ranar Dimokuradiyya: Dalilai 5 Da Suka Sa Ranar 12 Ga Watan Yuni Ke Da Muhimmanci A Tarihin Najeriya
A makon da ya gabata ne dai shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da dakatar da gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele daga muƙaminsa.
Sanarwar dai ta fito ne daga ofishin sakataren Gwamnatin Tarayya wacce daraktan yaɗa labarai na ofishin ya fitar.
Asali: Legit.ng