Abubuwa 6 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Tsohon Daraktan Ayyuka Na EFCC, Mohammed Abba
Mohammed Umar Abba, ya kasance tsohon daraktan ayyuka na hukumar yaki da cin hanci da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC).
A ranar Laraba, 14 ga watan Yuni ne sunan Umar Abba ya sake bayyana a kanen labarai bayan an kuskure shi a matsayin wanda zai zama mukaddashin shugaban hukumar EFCC bayan dakatar da Abdulrasheed Bawa, shugaban EFCC da Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi.
Sai dai kuma, an gano ba shine zai gaji Bawa ba domin dai ba shine daraktan ayyuka na hukumar mai ci ba kamar yadda aka dunga yayatawa.
Abba ya taba rike mukamin mukaddashin shugaban hukumar ta EFCC a lokacin da aka dakatar da tsohon mukaddashin shugaban hukumar, Ibrahim Magu a 2020.
Ga wasu abubuwa shida ya ya kamata ku sani game da tsohon daraktan ayyuka na hukumar EFCC:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. An haifi Mohammed Umar Abba a ranar 22 ga watan Yunin 1965 a karamar hukumar Tudunwada ta jihar Kano.
2. Abba ya yi digirinsa na farko a jami'ar Bayero, Kano. ya yi bautar kasarsa a hukumar yan sandan tsohuwar jihar Anambra sannan daga bisani ya samu shiga rundunar yan sandan Najeriya. Ya halarci makarantar yan sanda ta Kaduna, jihar Kaduna.
3. CP Abba ya samu amincewar hukumar a watan Janairun 2016 domin ya jagoranci sashin bincike na CTG1, wani bangare a hedkwata da ke Abuja.
4. An nada shi daraktan ayyuka na hukumar a 2017.
5. A 2019, an kara masa girma zuwa mukamin kwamishinan yan sanda.
6. A ranar 9 ga watan Yulin 2020, Abba ya zama mukaddashin shugaban hukumar, kasancewarsa jami'i mafi girma a sashin ayyuka lokacin da aka dakatar da tsohon shugaban EFCC, Ibrahim Magu.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da Abdulrasheed Bawa daga matsayin shugaban EFCC
A gefe guda, mun kawo a baya cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar yaki da cin hanci da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) har sai baba-ta-gani.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Willie Bassey, daraktan labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya ya saki a ranar Laraba, 14 ga watan Yuni.
Bassey ya ce dakatarwar da aka yi wa Bawa ya biyo bayan manyan zarge-zarge da ake yi masa na cin mutuncin kujerarsa.
Asali: Legit.ng