“Allah Ya Kiyaye Hanya Hajiya”: Bidiyon Matashiya Sanye Da Hijabi Tana Tuka Babbar Mota Ya Dauka Hankali

“Allah Ya Kiyaye Hanya Hajiya”: Bidiyon Matashiya Sanye Da Hijabi Tana Tuka Babbar Mota Ya Dauka Hankali

  • Bidiyon TikTok na wata matashiya Musulma tana tuka babbar mota ya yadu a dandalin TikTok
  • Bidiyon wanda ya dauka hankali, ya nuno lokacin da ta dare motar sannan ta tayar da injin dinta
  • Matar wacce ke sanye da hijabi ta tuka babbar motar cike da kwarewa da kwarin gwiwa wanda hakan ke nuna ita din gagaggiyar direba ce

Wani bidiyon TikTok na wata matashiya Musulma sanye da hijabinta tana tuka babbar mota hankali kwance ya ja hankali a soshiyal midiya.

Bidiyon ya nuna banbanci mai ban mamaki tsakanin shigarta da babbar motar yayin da ta hau kujerar direba sannan ta tayar da motar.

Matashiya na tuka babbar mota
“Allah Ya Kiyaye Hanya Hajiya”: Bidiyon Matashiya Sanye Da Hijabi Tana Tuka Babbar Mota Ya Dauka Hankali Hoto: @fatima364847474774
Asali: TikTok

Matashiya musulma tana tuka babbar mota

Matar ta rike sitiyarin babbar motar cike da kwarewa, tana mai nuna cewa ba wai kwararriyar direba bace ita kawai, ta san kan aikinta sosai.

Kara karanta wannan

“Rashawa Kiri-Kiri”: Babban Lauya Ya Caccaki Tsohon Sanata Kan Sakin Bakin Da Ya Yi a Zauren Majalisar Dattawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu amfani da soshiyal midiya da suka ci karo da bidiyon sun nuna mamakin cewa mace sanye da hijabi za ta iya tuka babbar mota cike da kwarewa sun kuma yaba mata.

Zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, bidiyon ya samu 'likes' 18,000 da martani fiye da dubu a TikTok.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Jndone ya yi martani:

"Akwai lokacin da ta kawo siminti zuwa wurinmu, tana kokari sosai."

@OgaZamfara ya ce:

"Ina kaunarki momina fatima shine suna mafi kyawu."

@MDGULAK442 ya rubuta:

"Allah ya kiyaye hanya hajiya ni daga Gulak MADAGALI."

@mlmimaryamfashlon ta yi martani:

"Abun da namiji zai iya yi mace ma za ta iya masha Allah."

@MubarakYunusHassan:

"Dan girman Allah ku bani number ta Allah yatsare."

@abubakarhamldu981:

"Ubangiji Allah ya tsare mu sharrin karfe."

Kara karanta wannan

"Sai Da Ya Yi Hawaye": Matashiya Ta Ba Direba Mai Kirki N10,000 Bayan Ya Caje Ta N2,500 Duk Da Tsadar Mai

@nllmazallanl891:

"Na shiga aljanna."

Yar shekaru 13 ta yashe iyayenta, ta buga wasanni da miliyan N40 da suka tara

A wani labari na daban, a wani lamari mai kama da al'mara, wata yarinya yar shekaru 13 daga China ta yi wa iyayenta bazata sakamakon dabi'antuwa da ta yi da buga wasanni ta intanet.

Matashiyar dai ta faki ido sannan ta dauke katin bankin mahaifiyarta inda ta dunga biyan kudin buga wasanni har ta kai ga cin miliyan N40 cikin watanni hudu kacal.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng