Ta Bayyana: Dalilin Da Yasa Shugaba Tinubu Ya Dakatar Da Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa

Ta Bayyana: Dalilin Da Yasa Shugaba Tinubu Ya Dakatar Da Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa

Gidan Gwamnati, Abuja - Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta yi bayani game da dalilin da yasa Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Abdulrasheed Bawa a matsayin shugaban Hukumar Yaki da Rashawa (EFCC).

Wata sanarwa da Willey Bassey, Darekta na sashin watsa labarai na ofishin SGF ya fitar ta ce Shugaba Tinubu ya dakatar da Bawa ne domin samun daman yin sahihin bincike kan ayyukan ofishinsa.

Tinubu ya dakata da shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa
Tinubu ya umurci a dakatar da shugaban EFCC, Bawa, don bincikarsa.
Asali: UGC

Akwai manyan zargin amfani da ofis ba ta hanyar da ta dace ba kan Bawa, in ji SGF

Sanarwar ta cigaba da cewa ana yi wa Bawa manyan zargin amfani da ofishinsa wurin aikata ba daidai ba, don haka za a yi bincike.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaban Kasa Tinubu Ya Dakatar Da Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa, Har Sai Baba-Ta-Gani

"Shugaba Bola Tinubu, GCFR, ya amince da cewa a dakatar da Mista Abdulrasheed Bawa nan take a matsayin shugaban Hukumar Yaki da Rashawa EFCC domin a samu damar yin cikakken bincike kan ayyukan da ya yi a ofishinsa," a cewar wani sashi na sanarwar.

An umurci Bawa ya mika jagoranci ga daraktan aikace-aikace

Kazalika, Legit.ng ta tattaro cewa an umurci Bawa ya mika jagorancin hukumar ga direktan sashin aikace-aikace na EFCC.

Diraktan zai cigaba da jagorancin harkokin hukumar har zuwa lokacin da za a kammala binciken da ake yi wa Bawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164