Yanzu Yanzu: Shugaban Kasa Tinubu Ya Dakatar Da Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa
- An dakatar da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Abdulrasheed Bawa
- Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da dakatar da Bawa sannan ya umurce shi da ya mika harkokin ofishinsa ga daraktan ayyuka a hukumar ta EFCC
- Dakatarwar da aka yi wa Bawa har sai baba-ta-gani ya biyo bayan zargin da ake masa na cin mutuncin kujerarsa
Shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar yaki da cin hanci da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), jaridar Daily Trust ta rahoto.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Willie Bassey, daraktan labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya ya saki a ranar Laraba, 14 ga watan Yuni.
A cewar Bassey, dakatarwar da aka yi wa Bawa ya biyo bayan manyan zarge-zarge da ake yi masa na cin mutuncin kujerarsa, rahoton TVC.
“Rashawa Kiri-Kiri”: Babban Lauya Ya Caccaki Tsohon Sanata Kan Sakin Bakin Da Ya Yi a Zauren Majalisar Dattawa
Bassey ya kuma bayyana cewa an yi dakatarwar ne domin bayar da damar bincike kan ayyukansa yayin da yake ofis.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Tinubu ya umurci Bawa da ya mika shugabanci ga daraktan ayyuka a EFCC
An umurci Bawa da ya gaggauta mika harkokin ofishinsa ga daraktan ayyuka a hukumar, wanda zai jagoranci lamuran ofishin shugaban hukumar har zuwa lokacin da za a kammala bincike.
"Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya amince da dakatar da Mista AbdulRasheed Bawa, CON, daga matsayin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) har sai baba-ta-gani domin bayar da damar bincike kan ayyukansa yayin da yake ofis.
"Hakan ya biyo bayan manyan zarge-zarge na cin mutuncin ofis da ake masa. An umurci Mista Bawa da ya gaggauta mika harkokin ofishinsa ga darakta, ayyuka a hukumar, wanda zai jagoranci harkokin ofishin shugaban hukumar har zuwa lokacin da za a kammala binciken.
Tinubu ya dakatar da gwamnan CBN, Godwin Emefiele
A wani labari makamancin wannan, mun ji a baya cewashugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).
Tinubu ya dakatar da Emefiele daga kujerarsa ne a ranar Juma'a, 9 ga watan Yuni, har zuwa lokacin da za a kammala bincike a kujerarsa.
Asali: Legit.ng